Sauran kwana biyu a yi Idin Ƙetarewa da idin abinci marar yisti, sai manyan firistoci da malaman Attaura suka nemi hanyar kama Yesu da makirci, su kashe shi,
Tun daga lokacin nan Yesu ya fara bayyana wa almajiransa, lalle ne ya tafi Urushalima, ya sha wuya iri iri a hannun shugabanni da manyan firistoci da malaman Attaura, har a kashe shi, a rana ta uku kuma a tashe shi.
Sarakunan suka ce wa sarki, “A kashe mutumin nan, gama yana karya zuciyar sojojin da suka ragu a birnin, da zuciyar sauran jama'a duka ta wurin irin maganganun da yake faɗa musu. Gama wannan mutum ba ya neman jin daɗin zaman wannan jama'a sai dai wahala yake nemar musu.”
Amma na tsauta musu, na ce, “Me ya sa kuka kwana a bayan garu? Idan kun ƙara yin haka zan kama ku.” Tun daga wannan lokaci ba su ƙara zuwa a ranar Asabar ba.
Daga wannan rana, sai rabin barorina suka yi ta gini, rabi kuwa suna riƙe da māsu, da garkuwoyi, da bakuna, da sulke. Shugabannin kuwa suka goyi bayan dukan Yahudawa sosai.