Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Yohanna 11:2 - Littafi Mai Tsarki

2 Maryamun nan kuwa, wadda ɗan'uwanta Li'azaru ba shi da lafiya, ita ce wadda ta shafa wa Ubangiji man ƙanshi, ta kuma shafe ƙafafunsa da gashinta.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 Maryamun nan kuwa, wadda ɗan’uwanta Lazarus yake rashin lafiya, ita ce ta zuba wa Ubangiji turare ta kuma goge ƙafafunsa da gashin kanta.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Yohanna 11:2
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai Maryamu ta ɗauko awo guda na man ƙanshi na nardi tsantsa, mai tamanin gaske, ta shafa a ƙafafun Yesu, sa'an nan ta shafe su da gashinta. Duk gidan ya game da ƙanshin man.


Yesu yana Betanya a gidan Saminu kuturu, yana cin abinci ke nan, sai ga wata mace ta zo da wani ɗan tulu na man ƙanshi na nardi tsantsa, mai tsadar gaske. Sai ta fasa ulun, ta tsiyaye masa man a kā.


Da Ubangiji ya gan ta, ya ji tausayinta, ya kuma ce mata, “Daina kuka.”


Sai Yahaya ya kira almajiransa biyu, ya aike su gun Ubangiji yana tambaya, “Kai ne mai zuwan nan, ko kuwa mu sa ido ga wani?”


To, 'yan'uwan nan mata suka aika masa, suka ce, “Ya Ubangiji, ga shi, wanda kake ƙaunan nan ba shi da lafiya.”


Sai Marta ta ce wa Yesu, “Ya Ubangiji, da kana nan da ɗan'uwana bai mutu ba.


Da Maryamu ta iso inda Yesu yake, ta gan shi, sai ta faɗi a gabansa ta ce masa, “Ya Ubangiji, da kana nan da dan'uwana bai mutu ba.”


Kuna kirana Malam, da kuma Ubangiji. Daidai ne kuwa, don haka nake.


Tun da yake ni Ubangijinku da kuma Malaminku, har na wanke muku ƙafa, ashe, ku ma wajibi ne ku wanke wa juna.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ