Suna kama da karnuka masu zarin ci, ba su taɓa samun abin da ya ishe su ba. Makiyayan nan kuma ba haziƙai ba ne, dukansu, kowa ya nufi inda ya ga dama. Kowa yana ta nemar wa kansa riba.
Kakanninmu a Masar Ba su fahimci ayyukan Allah masu banmamaki ba, Sau da yawa sukan manta da irin ƙaunar da ya nuna musu, Suka tayar wa Mai Iko Dukka a Bahar Maliya.
Mun kuma sani Ɗan Allah ya zo, ya yi mana baiwar fahimta domin mu san shi wanda yake na gaskiya. Mu kuwa muna a cikinsa, shi da yake na gaskiya, wato Ɗansa Yesu Almasihu. Shi ne Allah na gasikya da kuma rai madawwami.
Mutumin da ba shi da Ruhu yakan ƙi yin na'am da al'amuran Ruhun Allah, don wauta ne a gare shi, ba kuwa zai iya fahimtarsu ba, domin ta wurin ruhu ne ake rarrabewa da su.
Ai kuwa, karin maganar nan na gaskiya ya dace da su cewa, “Kare ya cinye amansa,” da kuma, “Gursunar da aka yi wa wanka ta kome ga birgima cikin laka.”