Don haka, Yahudawa suka ƙara nema su kashe shi, ba don ya keta Asabar kaɗai ba, har ma domin ya ce Allah Ubansa ne, wato, yana daidaita kansa da Allah.
Dawuda kuwa ya damu ƙwarai gama mutane suna niyyar su jajjefe shi da duwatsu, domin ransu ya ɓace saboda 'ya'yansu mata da maza. Amma Ubangiji Allahnsa ya ƙarfafa shi.
A cikin annabawa wane ne kakanninku ba su tsananta wa ba? Sun kuma kashe waɗanda suka yi faɗi a kan zuwan Mai Adalcin nan, wanda a yanzu kuka zama maciya amanarsa, da kuma makasansa,
Don alhakin jinin dukan adalai da aka zubar a duniya yă komo a kanku, tun daga jinin Habila adali, har ya zuwa na Zakariya ɗan Berikiya, wanda kuka kashe a tsakanin Haikalin da bagaden hadaya.