Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Yohanna 10:28 - Littafi Mai Tsarki

28 Ina ba su rai madawwami, ba kuwa za su halaka ba har abada, ba kuma mai ƙwace su daga hannuna.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

28 Ina ba su rai madawwami, ba za su taɓa hallaka ba; ba kuma mai ƙwace su daga hannuna.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Yohanna 10:28
60 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Duk wanda Uba ya ba ni zai zo gare ni, wanda kuwa ya zo gare ni ba zan kore shi ba ko kaɗan.


Saboda haka, yana da ikon ceton masu kusatowa ga Allah ta wurinsa, matuƙar ceto, tun da yake kullum a raye yake saboda yi musu addu'a.


Waɗanda Allah ya riga ya zaɓa tun tuni, su ne ya ƙaddara su ɗauki kamannin Ɗansa, domin shi Ɗan yă zama na farko a cikin 'yan'uwa masu yawa.


Wannan kuwa domin a cika maganar da ya yi ne cewa, “A cikin waɗanda ka ba ni ban yar da ko ɗaya ba.”


Na tabbata shi wanda ya fara kyakkyawan aiki a gare ku, zai ƙarasa shi, har ya zuwa ranar Yesu Almasihu.


Amma ba makamin da aka ƙera da ya isa ya cuce ki, Za ki iya amsa wa dukan waɗanda za su yi ƙararki. Zan kāre bayina, In kuwa ba su nasara.” Ubangiji ne ya faɗa.


Wannan shi ne alkawarin da ya yi mana, wato, rai madawwami.


Amma duk wanda ya sha ruwan da zan ba shi, ba zai ƙara jin ƙishirwa ba har abada. Ruwan da zan ba shi kuwa zai zama maɓuɓɓuga a gare shi, yana ɓuɓɓugowa har ya zuwa rai madawwami.”


Saboda haka a yanzu, ba sauran kayarwa ga waɗanda suke na Almasihu Yesu.


Ga wanda yake da iko yă tsare ku daga faɗuwa, yă kuma miƙa ku marasa aibi a gaban ɗaukakarsa da matuƙar farin ciki,


tun da ka ba shi iko a kan dukkan 'yan adam, yă ba da rai madawwami ga duk waɗanda ka ba shi.


Lalle hakika, ina gaya muku, duk mai jin maganata, yake kuma gaskata wanda ya aiko ni, yana da rai madawwami. Ba za a yi masa hukunci ba, domin ya riga ya tsere wa mutuwa, ya kai ga rai.


Sun dai fita daga cikinmu, amma dā ma can ba namu ba ne. Don in da namu ne, da har yanzu suna tare da mu. Amma sun fita ne domin a bayyana dukansu ba namu a ciki.


Wannan kuma ita ce shaidar, cewa Allah yā ba mu rai madawwami, wannan rai kuwa yana cikin Ɗansa.


Ku tsaya a kan ƙaunar da Allah yake yi mana, kuna sauraron jinƙan Ubangijinmu Yesu Almasihu mai kaiwa ga rai madawwami.


wato, ku da ikon Allah yake kiyayewa ta wurin bangaskiyarku, domin samun ceton nan da aka shirya a bayyana a ƙarshen zamani.


Gama Ubangiji yana ƙaunar abin da yake daidai, Ba ya rabuwa da amintattun jama'arsa, Yana kiyaye su koyaushe, Amma za a kori zuriyar mugaye.


Hakika, yana ƙaunar jama'arsa, Dukan tsarkaka suna a ikonka, Suna biye da kai, Suna karɓar umarninka.


Amma Ubangiji ya ceci Isra'ila, Nasararsa kuwa za ta tabbata har abada, Mutanensa ba za su taɓa shan kunya ba.


Yesu ya ce mata, “Ai, ni ne tashin matattu, ni ne kuma rai. Wanda ya gaskata da ni, ko ya mutu zai rayu.


Ubangiji ya bayyana gare ni tun daga nesa cewa, “Ya Isra'ila, budurwa! Na kusace ki da madawwamiyar ƙaunata, Ba zan fasa amintacciyar ƙaunata a gare ki ba. Zan sāke gina ki, Za ki kuwa ginu, Za ki ɗauki kayan kaɗe-kaɗe, Za ki shiga rawar masu murna.


Daga Yahuza bawan Yesu Almasihu, ɗan'uwan Yakubu zuwa ga kirayayyu, ƙaunatattun Allah Uba, keɓaɓɓu ga Yesu Almasihu.


Ko sau nawa amintaccen mutum ya faɗi, ba abin damuwa ba ne, gama a ko yaushe zai sāke tashi, amma masifa takan hallaka mugaye.


Ya ku 'yan'uwa, ƙaunatattun Ubangiji, lalle ne kullum mu gode wa Allah saboda ku, domin Allah ya zaɓe ku, don ku fara samun ceto ta wurin tsarkakewar Ruhu, da kuma amincewarku da gasikya.


Wanda ya gaskata da Ɗan, yana da rai madawwami. Wanda ya ƙi bin Ɗan kuwa, ba zai sami rai ba, sai dai fushin Allah ya tabbata a gare shi.”


Saboda haka, ne nake shan wuya haka. Duk da haka, ban kunyata ba, domin na san wanda na gaskata da shi, na kuma tabbata yana da iko ya kiyaye abin da na danƙa masa, har ya zuwa waccan rana.


Wato kamar yadda mallakar zunubi mutuwa ce, haka mallakar Allah ta wurin alheri adalci ce, da take bi da mu zuwa rai madawwami ta wurin Yesu Almasihu Ubangijinmu.


Har su ma da suke cewa su mutanen kirki ne Suna ƙara tabbatarwa ba su yi kuskure ba.


Duk da haka an yi mini jinƙai musamman, don ta kaina, ni babbansu, Yesu Almasihu yă nuna cikakken haƙurinsa, in zama gurbi ga waɗanda a nan gaba za su gaskata da shi su sami rai madawwami.


Gama sakamakon zunubi mutuwa ne, amma baiwar Allah ita ce rai madawwami a cikin Almasihu Yesu Ubangijinmu.


In kuwa saboda laifin mutum ɗayan nan ne mutuwa ta yi mallaka ta wurinsa, ashe kuwa, waɗanda suke samun alherin nan mayalwaci, da kuma baiwar nan ta adalcin Allah, sai su yi mallaka fin haka ƙwarai a cikin rai, ta wurin ɗayan nan, wato Yesu Almasihu.


Ta wurinsa kuma muka sami shiga alherin nan da muke a ciki, saboda bangaskiyarmu, muna kuma taƙama da sa zuciyarmu ga samun ɗaukakar nan ta Allah.


Suna ta jifan Istifanas, shi kuwa yana ta addu'a, yana cewa, “Ya Ubangiji Yesu, ka karɓi ruhuna.”


Saura ɗan lokaci kaɗan duniya ba za ta ƙara ganina ba, amma ku za ku gan ni. Saboda ni a raye nake, ku ma za ku rayu.


Lalle hakika ina gaya muku, wanda ya ba da gaskiya, yana da rai madawwami.


Kada ku yi wahala a kan neman abinci mai lalacewa, sai dai a kan abinci mai dawwama har ya zuwa rai madawwami, wanda Ɗan Mutum zai ba ku. Domin shi ne wanda Uba, wato Allah, ya tabbatar wa da ikon yin haka.”


Zan yi madawwamin alkawari da su, ba zan fasa nuna musu alheri ba, zan kuwa sa tsorona a zukatansu domin kada su bar bina.


“Zai kiyaye rayukan amintattun mutanensa, Amma mugayen mutane za su lalace cikin duhu, Ba ƙarfin mutum yake sa ya yi nasara ba.


To, tun da yake a yanzu an kuɓutar da mu ta wurin jininsa, ashe kuwa, ta wurinsa za mu fi samun kārewa daga fushin Allah ke nan.


Bitrus ya amsa masa ya ce, “Ya Ubangiji, gun wa za mu je? Kai kake da maganar rai madawwami.


Sai Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Ya Uba, na sa ruhuna a ikonka.” Da ya faɗi haka kuwa, sai ya cika.


Mutum ba zai ƙara koya wa maƙwabcinsa, ko ɗan'uwansa cewa, ‘Ka san Ubangiji’ ba, gama su duka za su san ni, tun daga ƙarami har zuwa babba. Zan gafarta musu laifofinsu, ba kuwa zan ƙara tunawa da zunubansu ba.”


Hanyar da adalai suke bi kamar fitowar rana ce, sai ta yi ta ƙara haske, har ta take tsaka.


Ina ba da kaina gare ka domin ka kiyaye ni. Za ka fanshe ni, ya Ubangiji, Kai Allah mai aminci ne.


Don almasihan ƙarya da annabawan ƙarya za su firfito, su nuna alamu da abubuwan al'ajabi, don su ɓad da ko da zaɓaɓɓu ma, in zai yiwu.


“Ku mutanena, ku kasa kunne yanzu, ku zo gare ni, Ku zo gare ni, za ku kuwa sami rai! Zan yi tabbataccen alkawari da ku, Zan sa muku albarkun da na alkawarta wa Dawuda.


ya ce, “Ina tsaronta ina yi mata banruwa kowane lokaci, ina tsaronta dare da rana, don kada a yi mata ɓarna.


Zan sa makiyayan da za su lura da su. Ba kuwa za su ƙara jin tsoro, ko razana ba, ba kuma wanda zai ɓace, ni Ubangiji na faɗa.


Ubana, wanda ya ba ni su, ya fi duka girma, ba kuwa mai iya ƙwace su daga ikon Uban.


wannan Rai kuwa an bayyana shi, mu kuwa mun gani, muna ba da shaida, muna kuma sanar da ku Rai madawwamin nan wanda tun dā yake tare da Uba, aka kuwa bayyana shi gare mu,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ