Ku kula da kanku, da kuma duk garken da Ruhu Mai Tsarki ya sa ku ku zama masu kula da shi, kuna kiwon Ikkilisiyar Allah wadda ya sama wa kansa da jininsa.
Allah mai zartar da salama, wanda ya ta da Ubangijinmu Yesu, Makiyayin tumaki mai girma, daga matattu, albarkacin jinin nan na tabbatar madawwamin alkawari,
Masu sayensu za su yanyanka su, ba za a kuwa hukunta su ba. Masu sayar da su kuma za su yi hamdala gare ni, su ce sun sami dukiya. Makiyayansu kuwa ba su ji tausayinsu ba.
Asirtacciyar ma'anar taurarin nan bakwai da ka gani a hannuna na dama kuwa, da kuma fitilun nan bakwai na zinariya, to, su taurarin nan bakwai, mala'iku ne na ikilisiyoyin nan bakwai, fitilun nan bakwai kuwa, ikkilisiya bakwai ɗin ne.
Wannan shi ya sa na bar ka a Karita, musamman domin ka ƙarasa daidaita al'amuran da suka saura, ka kuma kafa dattawan ikkilisiya a kowane gari, kamar yadda na nushe ka,
“Ka farka, ya kai takobi, ka fāɗa wa makiyayina, Ka fāɗa wa mutumin da yake kusa da ni, Ka sari makiyayin domin tumakin su watse. Zan bugi ƙanana da hannuna, Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.
Zai zama salamarmu. Sa'ad da kuma Assuriyawa za su kawo mana yaƙi, Za su tattake kagaranmu, Za mu sa makiyaya bakwai da shugabanni takwas su yi gāba da su.
Amma suka tuna da zamanin dā, zamanin Musa bawan Ubangiji, suka yi tambaya suka ce, “Yanzu fa, ina Ubangiji yake wanda ya ceci shugabannin jama'arsa daga teku? Ina Ubangiji yake, wanda ya ba Musa iko musamman?