Duk da haka, ƙaƙƙarfan harsashin ginin nan na Allah ya tabbata, hatimin nan kuwa yana jikinsa cewa, “Ubangiji ya san nasa,” da kuma, “Duk wanda ya bayyana yarda ga sunan Ubangiji, to, yă yi nesa da aikata mugunta.”
Mun kuma sani Ɗan Allah ya zo, ya yi mana baiwar fahimta domin mu san shi wanda yake na gaskiya. Mu kuwa muna a cikinsa, shi da yake na gaskiya, wato Ɗansa Yesu Almasihu. Shi ne Allah na gasikya da kuma rai madawwami.
“ ‘Na san ayyukanka, da famarka, da jimirinka, da yadda ba ka iya haƙurce wa mugaye, ka kuma gwada waɗanda suke ce da kansu manzanni, alhali kuwa ba su ba ne, ka tarar na ƙarya ne.
Saboda haka, ne nake shan wuya haka. Duk da haka, ban kunyata ba, domin na san wanda na gaskata da shi, na kuma tabbata yana da iko ya kiyaye abin da na danƙa masa, har ya zuwa waccan rana.
Dahir na ɗauki dukkan abubuwa hasara ne, a kan mafificiyar darajar sanin da nake yi na Almasihu Yesu Ubangijina. Saboda shi ne na zaɓi yin hasarar dukkan abubuwa, har ma na mai da su tozari domin Almasihu yă zama nawa,
“ ‘Na san a inda kake da zama, wato, a inda kursiyin Shaiɗan yake. Duk da haka kuwa, ka tsaya a gare ni, ba ka bar yi mini bangaskiya ba, ko a zamanin Antibas amintaccen mashaidina, wanda aka kashe a cikinku, a inda Shaiɗan yake zaune.
Domin shi Allah wanda ya ce, “Haske yă ɓullo daga duhu ya haskaka,” shi ne ya haskaka zukatanmu domin a haskaka mutane su san ɗaukakarsa a fuskar Yesu Almasihu.
“ ‘Na san ayyukanka. Ka ga, na bar maka ƙofa a buɗe, wadda ba mai iya rufewa. Na dai san ƙarfinka kaɗan ne, duk da haka, kā kiyaye maganata, ba ka yi musun sanin sunana ba.
“ ‘Na san tsananin da kake sha, da talaucinka (amma bisa ga hakika kai mawadaci ne), na kuma san yanken da waɗansu suke yi maka, masu cewa su Yahudawa ne, alhali kuwa ba su ba ne, jama'ar Shaiɗan ne.
Bayan shan wahalarsa, zai sāke yin murna, Zai fahimta wahalar da ya sha ba ta banza ba ce, Shi ne bawana, adali, Zai ɗauki hukuncin mutane masu yawa, Ya sa su zama mutanena amintattu.
“Ka kuma rubuta wa mala'ikan ikkilisiyar da take a Sardisu haka, ‘Ga maganar mai Ruhohin Allah guda bakwai, da kuma taurarin nan bakwai. “ ‘Na san ayyukanka, kai rayayye ne, alhali kuwa matacce ne kai.