Har wa yau sabon umarni nake rubuto muku, wanda yake tabbatacce ga Almasihu, da kuma gare ku, domin duhu yana shuɗewa, hakikanin haske kuma yana haskakawa.
Ubangiji ya ce mini, “Bawana, ina da aiki mai girma dominka, Ba komo da girman jama'ar Isra'ila da suka ragu kaɗai ba, Amma zan sa ka zama haske ga al'ummai, Domin dukan duniya ta tsira.”
Mun kuma sani Ɗan Allah ya zo, ya yi mana baiwar fahimta domin mu san shi wanda yake na gaskiya. Mu kuwa muna a cikinsa, shi da yake na gaskiya, wato Ɗansa Yesu Almasihu. Shi ne Allah na gasikya da kuma rai madawwami.
Ga amsar da za ku ba su, ku ce, “Ku kasa kunne ga koyarwar Ubangiji. Kada ku kasa kunne ga 'yan bori. Gama abin da suka faɗa muku ba zai amfane ku ba.”