A kan wannan ga abin da Ubangiji Mai Runduna ya amsa, ya ce, “Zan aiki manzona don ya shirya mini hanya, sa'an nan Ubangiji wanda kuke nema zai zo farat ɗaya a cikin Haikalinsa. Manzon da kuke sa zuciyar zuwansa, yana zuwa, zai yi shelar alkawarina.”
Dā kam, ban san shi ba, sai dai wanda ya aiko ni in yi baftisma da ruwa, shi ne ya ce mini, ‘Wanda ka ga Ruhun na sauko masa, yana kuma kasance a kansa, shi ne mai yin baftisma da Ruhu Mai Tsarki.’
To, baftismar da Yahaya ya yi, daga ina take? Daga Sama take, ko kuwa ta mutum ce?” Sai suka yi ta muhawwara da juna, suna cewa, “In muka ce, ‘Daga Sama take,’ sai ya ce mana, ‘To, don me ba ku gaskata shi ba?’