Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Yohanna 1:51 - Littafi Mai Tsarki

51 Yesu kuma ya ce masa, “Lalle hakika, ina gaya muku, za ku ga sama ta dāre, mala'ikun Allah suna hawa da sauka ga Ɗan Mutum.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

51 Sai ya ƙara da cewa, “Gaskiya nake gaya muku, za ku ga sama a buɗe, mala’ikun Allah kuma suna hawa suna kuma sauka a kan Ɗan Mutum.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Yohanna 1:51
55 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ya yi mafarki, ga wani tsani tsaye daga ƙasa, kansa ya kai sama, sai ga mala'ikun Allah suna hawa da sauka ta kansa!


Sai ya ce, “Ga shi, ina ganin sama a buɗe, da kuma Ɗan Mutum tsaye dama ga Allah.”


[Sai wani mala'ika ya bayyana a gare shi daga Sama, yana ƙarfafa shi.


Ba labari sai ga taron rundunar Sama tare da mala'ikan nan, suna yabon Allah, suna cewa,


Yesu ya ce, “Ni ne. Za ku kuwa ga Ɗan Mutum zaune dama ga Mai Iko, yana kuma zuwa cikin gajimare.”


Da fitowarsa daga ruwan sai ya ga sama ta dāre, Ruhu yana sauko masa kamar kurciya.


Da aka yi wa Yesu baftisma, nan da nan da ya fito daga ruwan, sai ga sama ta dāre, ya ga Ruhun Allah na saukowa kamar kurciya, har ya sauka kansa.


A ranar biyar ga watan huɗu, a shekara ta talatin, ina cikin waɗanda aka kai su bautar talala, muna kusa da kogin Kebar, sai aka buɗe mini sammai, na kuwa ga wahayi na ɗaukakar Allah.


ya ga sama ta dare, wani abu kuma yana saukowa kamar babban mayafi, ana zuro shi ƙasa ta kusurwoyinsa huɗu.


To, da aka yi wa dukan mutane baftisma, Yesu ma aka yi masa baftisma, yana addu'a ke nan, sai sama ta dāre,


Sa'an nan Iblis ya rabu da shi. Sai ga mala'iku sun zo suna yi masa hidima.


Sai na ga sama ta dāre, sai ga wani farin doki! Mahayinsa kuwa ana ce da shi Amintacce, Mai Gaskiya, yana hukunci da adalci, yana kuma yaƙi.


Bayan wannan na duba, sai ga wata ƙofa a buɗe a Sama. Muryar farko da na ji dā, mai kama da ƙaho, ta ce mini, “Hawo nan, zan nuna maka abin da lalle ne ya auku bayan wannan.”


yă kuma ba ku hutu har da mu ma, ku da ake ƙuntata wa ɗin, a ranar bayyanar Ubangiji Yesu daga Sama tare da manyan mala'ikunsa, a cikin wuta mai ruruwa,


Sai ga wani mala'ikan Ubangiji tsaye kusa da su, ɗaukakar Ubangiji kuma ta haskaka kewayensu, har suka tsorata gaya,


Ashe, dukan mala'iku ba ruhohi masu hidima ba ne, waɗanda Allah yakan aika, don su yi wa waɗanda za su gāji ceto hidima?


Ba shakka, asirin addininmu muhimmi ne ƙwarai, An bayyana shi da jiki, Ruhu ya nuna shi adali ne, Mala'iku sun gan shi, An yi wa al'ummai wa'azinsa, An gaskata da shi a duniya, An ɗauke shi Sama wurin ɗaukaka.


“Lalle hakika, ina gaya muku, wanda bai shiga garken tumaki ta ƙofa ba, amma ya haura ta wani gu, to, shi ɓarawo ne, ɗan fashi kuma.


Amma nan gaba, Ɗan Mutum zai zauna dama na Allah Mai iko.”


“Sa'ad da Ɗan Mutum ya zo cikin ɗaukakarsa tare da mala'iku duka, sa'an nan ne zai zauna a maɗaukakin kursiyinsa.


Anuhu ma wanda yake na bakwai daga Adamu, shi ma ya yi annabci a kan waɗannan mutane cewa, “Ga shi, Ubangiji ya zo da dubban tsarkakansa,


Za su sha hukuncin madawwamiyar hallaka, suna a ware da zatin Ubangiji, da kuma, maɗaukakin ikonsa,


“Lalle hakika, ina gaya muku, duk wanda yake gaskatawa da ni ayyukan da nake yi shi ma haka zai yi. Har ma, zai yi ayyukan da suka fi waɗannan, domin zan tafi wurin Uba.


Lalle hakika ina gaya muku, wanda ya ba da gaskiya, yana da rai madawwami.


Tun suna cikin damuwa da abin, sai kawai ga waɗansu mutum biyu a tsaye kusa da su, saye da tufafi masu ƙyalƙyali.


Ɗan Mutum zai tafi ne, yadda labarinsa yake a rubuce, duk da haka kaiton mutumin nan da yake ba da Ɗan Mutum! Da ma ba a haifi mutumin nan ba, da zai fiye masa.”


Lalle hakika, ina gaya maka, lokacin samartakarka kakan yi wa kanka ɗamara, ka tafi inda ka nufa, amma in ka tsufa, za ka miƙe hannuwanka, wani ya yi maka ɗamara, ya kai ka inda ba ka nufa ba.”


Lalle hakika, ina gaya muku, kowa ya kiyaye maganata ba zai mutu ba har abada.”


Sa'an nan Yesu ya ce musu, “Lalle hakika, ina gaya muku, ba Musa ne ya ba ku gurasar nan daga Sama ba, Ubana ne yake ba ku hakikanin Gurasa daga Sama.


Yesu ya amsa masa ya ce, “Lalle hakika, ina gaya maka, in ba an haifi mutum ta ruwa da kuma Ruhu ba, ba zai iya shiga Mulkin Allah ba.


Lalle hakika, ina gaya muku, za ku yi kuka da kuma gunji, amma duniya za ta yi farin ciki. Za ku yi baƙin ciki, amma baƙin cikinku zai koma farin ciki.


Lalle hakika, ina gaya muku, bawa ba ya fin ubangijinsa, manzo kuma ba ya fin wanda ya aiko shi.


Don haka Yesu ya sāke ce musu, “Lalle hakika, ina gaya muku, ni ne ƙofar tumakin.


Sai Yesu ya ce musu, “Lalle hakika, ina gaya muku, in ba ku ci naman jikin Ɗan Mutum ba, kuka kuma sha jininsa, ba rai a gare ku.


Ya kuma ba shi ikon zartar da hukunci, saboda shi Ɗan Mutum ne.


Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Lalle hakika, ina gaya muku, Ɗan ba ya yin kome shi kaɗai, sai abin da ya ga Uba yana yi. Domin duk abin da Uban yake yi, haka shi Ɗan ma yake yi.


Yesu ya amsa masa ya ce, “Lalle hakika, ina gaya maka, in ba a sāke haifar mutum ba, ba zai iya ganin Mulkin Allah ba.”


Amma domin ku sakankance Ɗan Mutum yana da ikon gafarta zunubi a duniya” sai ya ce wa shanyayyen, “Tashi, ka ɗauki shimfiɗarka ka tafi gida.”


Yesu ya ce masa, “Yanyawa da ramummukansu, tsuntsaye kuma da sheƙunan, amma Ɗan Mutum ba shi da wurin shaƙatawa.”


“Ka farka, ya kai takobi, ka fāɗa wa makiyayina, Ka fāɗa wa mutumin da yake kusa da ni, Ka sari makiyayin domin tumakin su watse. Zan bugi ƙanana da hannuna, Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.


A ran nan, ba za ku yi mini wata tambaya ba. Lalle hakika, ina gaya muku, kome kuka roƙi Uba zai ba ku saboda sunana.


Yesu ya amsa ya ce, “Ashe, za ka ba da ranka saboda ni? Lalle hakika, ina gaya maka, kafin zakara ya yi cara, za ka yi musun sanina sau uku.”


Sai Yesu ya ce musu, “Lalle hakika, ina gaya muku, tun ba a haifi Ibrahim ba, ni ne.”


Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Lalle hakika, ina gaya muku, duk mai aikata zunubi bawan zunubi ne.


Yesu ya amsa musu ya ce, “Lalle hakika, ina gaya muku, kuna nemana ne ba don kun ga mu'ujizai ba, sai don kun ci gurasar nan kun ƙoshi.


Yesu ya amsa ya ce, “Wato, domin na ce maka na gan ka a gindin ɓaure ne kake ba da gaskiya? Ai, za ka ga al'amuran da suka fi haka ma.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ