37 Almajiran nan biyu suka ji ya faɗi haka, sai suka bi Yesu.
37 Da almajiran nan biyu suka ji ya faɗi haka, sai suka bi Yesu.
Ashe, bangaskiya ta wurin jawabin da ake ji take samuwa, jawabin da ake ji kuma ta Maganar Almasihu yake.
Kashegari Yesu ya yi niyyar zuwa ƙasar Galili. Sai ya sami Filibus, ya ce masa, “Bi ni.”
Ruhu da amarya suna cewa, “Zo.” Duk wanda ya ji kuwa, yă ce, “Zo.” Duk mai jin ƙishirwa ya zo, duk mai bukata, yă ɗibi ruwan rai kyauta.
Mutanen wani birni za su tafi wurin mutanen wani birni, su ce musu, ‘Za mu tafi mu roƙi alherin Ubangiji, mu kuma nemi Ubangiji Mai Runduna. Ku zo mu tafi.’
Kada wata alfasha ta fita daga bakinku, sai dai irin maganar da ta kyautu domin ingantawa, a kuma yi ta a kan kari, domin ta sa alheri ga masu jinta.
Me ya fi wannan zama abin murna? Mutum ya sami maganar da take daidai a lokacin da ya dace!
Yana duban Yesu na tafiya, sai ya ce, “Kun ga, ga Ɗan Rago na Allah!”
Yesu ya waiwaya ya ga suna biye da shi, sai ya ce musu, “Me kuke nema?” Suka ce masa, “Ya Rabbi, wato Malam ke nan, ina kake da zama?”