35 Kashegari kuma Yahaya na tsaye da almajiransa biyu.
35 Kashegari kuma Yohanna yana can tare da biyu daga cikin almajiransa.
Sa'an nan mutane waɗanda suke tsoron Ubangiji suka yi magana da junansu, Ubangiji kuwa ya kasa kunne ya ji abin da suke cewa. A gabansa aka rubuta a littafin tarihin waɗanda suke tsoron Ubangiji, suna kuwa girmama shi.
Kashegari Yahaya ya tsinkayo Yesu na nufo shi, sai ya ce, “Kun ga, ga Ɗan Rago na Allah, wanda zai ɗauke zunubin duniya!
Kashegari Yesu ya yi niyyar zuwa ƙasar Galili. Sai ya sami Filibus, ya ce masa, “Bi ni.”
A rana ta uku sai aka yi bikin aure a Kana ta ƙasar Galili. Uwar Yesu kuwa tana nan,