24 Su kuwa, Farisiyawa ne suka aiko su.
24 To, waɗansu Farisiyawan da aka aika
Da ya fito daga wurin, sai malaman Attaura da Farisiyawa suka fara matsa masa ƙwarai, suna tsokanarsa ya yi maganar abubuwa da yawa,
Farisiyawa kuwa da yake masu son kuɗi ne, da jin haka, suka yi masa tsaki.
Amma Farisiyawa da masanan Attaura suka shure abin da Allah yake nufinsu da shi, da yake sun ƙi ya yi musu baftisma.
Sun sani tun ainihi, in dai za su yarda su yi shaida, cewa lalle ni Bafarisiye ne bisa ga ɗariƙar nan da ta fi tsanani cikin addinin nan namu.
Sadukiyawa sun ce, wai ba tashin matattu, ba kuma mala'iku, ko ruhu. Farisiyawa kuwa sun tsaya a kan cewa duk akwai.
Kai makahon Bafarisiye! Sai ka fara tsarkake cikin ƙwaryar da akushin don bayansu ma ya tsarkaka.
Ya ce, “Ni murya ce ta mai kira a jeji, mai cewa, ‘Ku miƙe wa Ubangiji tafarki,’ yadda Annabi Ishaya ya faɗa.”
Sai suka tambaye shi suka ce, “To, don me kake yin baftisma in kai ba Almasihu ba ne, ba kuwa Iliya ba, ba kuma annabin nan ba?”