2 Shi ne tun fil'azal yake tare da Allah.
2 Yana nan tare da Allah tun farar farawa.
A sa'ad da Allah ya fara halittar Sama da duniya,
Ina kusa da shi kamar mai tsara fasalin gini, Ni ce abar murnarsa kowace rana, A ko yaushe ina farin ciki a gabansa.
Tun fil'azal akwai Kalma, Kalman nan kuwa tare da Allah yake, Kalman nan kuwa Allah ne.
Dukan abubuwa sun kasance ta gare shi ne, ba kuma abin da ya kasance na abubuwan da suka kasance, sai ta game da shi.
Idan na ce, ‘Ba zan ambaci Ubangiji ba, Ban zan ƙara yin magana da sunansa ba,’ Sai in ji damuwa a zuciyata, An kulle ta a ƙasusuwana, Na gaji da danne ta a cikina, Ba zan iya jurewa ba.