Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Yaƙub 5:9 - Littafi Mai Tsarki

9 'Yan'uwa, kada ku yi wa juna gunaguni, don kada a hukunta ku. Ga mai shari'a a bakin ƙofa!

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 ’Yan’uwa, kada ku yi gunaguni da juna, don kada a hukunta ku. Alƙalin yana tsaye a bakin ƙofa!

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Yaƙub 5:9
21 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Kada ya ɗaukar wa kansa fansa a kan wani ko ya yi ta ƙinsa, amma ya ƙaunaci sauran mutane kamar yadda yake ƙaunar kansa. Ni ne Ubangiji.


Don haka, kada ku yanke wani hukunci tun lokaci bai yi ba, kafin komowar Ubangiji, wanda zai tone al'amuran da suke ɓoye a duhu, ya kuma bayyana nufin zukata. A sa'an nan ne, Allah zai yaɓa wa kowa daidai gwargwado.


Ya ku 'yan'uwana, kada ku kushe wa juna. Kowa ya kushe wa ɗan'uwansa, ko ya ɗora masa laifi, ya kushe wa shari'a ke nan, ya kuma ɗora mata laifi. In kuwa ka ɗora wa shari'a laifi, kai ba mai binta ba ne, mai ɗora mata laifi ne.


Haka kuma in kun ga duk waɗannan abubuwa, ku sani ya kusato, a bakin ƙofa ma yake.


Ku riƙa yi wa juna baƙunta, ba tare da ƙunƙuni ba.


In da ka yi daidai, ai, da ka yi murmushi. Amma tun da ka yi mugunta, to, zunubi zai yi fakonka don ya rinjaye ka kamar naman jeji. Yana so ya mallake ka, amma tilas ne ka rinjaye shi.”


Kada mu zama masu homa, muna tsokanar juna, muna yi wa juna hassada.


Amma lalle su ba da hujjojinsu ga wannan da yake a shirye ya yi wa rayayyu da matattu shari'a.


Don duk Shari'a an ƙunshe ta ne a kalma guda, wato, “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.”


To, duk wannan ya same su ne a kan misali, an kuma rubuta shi ne don a gargaɗe mu, mu da ƙarshen zamani ya zo mana.


Haka kuma sa'ad da kuka ga waɗannan abubuwa na aukuwa, ku sani ya kusato, a bakin ƙofa ma yake,


Sai kowa yă bayar yadda ya yi niyya, ba tare da ɓacin rai ko tilastawa ba, domin Allah yana son mai bayarwa da daɗin rai.


Hirudiya kuwa na riƙe da Yahaya cikin zuciyarta, har ta so ta kashe shi, amma ba ta sami hanya ba,


Suna kai da kawowa ko'ina neman abinci, In ba su sami abin da ya ishe su ba, Sukan yi gunaguni.


Ga ni nan a tsaye a bakin ƙofa, ina ƙwanƙwasawa, kowa ya ji muryata ya buɗe ƙofar, sai in shiga wurinsa, in ci abinci tare da shi, shi kuma tare da ni.


“Lokaci ya yi, ranar ta gabato, kada mai saye ya yi farin ciki, kada kuma mai sayarwa ya yi baƙin ciki, gama fushina yana kan taron jama'a duka.


Mai ba da Shari'a ɗaya ne, shi ne kuma mai yinta, shi ne kuwa mai ikon ceto da hallakarwa. To, kai wane ne har da za ka ɗora wa ɗan'uwanka laifi?


Domin haka, sai ku yi haƙuri, 'yan'uwana, har ya zuwa ranar komowar Ubangiji. Ga shi, manomi yana sa rai ga samun amfanin gona mai albarka, yana kuwa haƙuri da samunsa, har a yi ruwan shuka da na kaka.


A kan misalin shan wuya da haƙuri kuma, 'yan'uwa, ku dubi annabawa ma da suka yi magana da sunan Ubangiji.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ