Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Yaƙub 5:8 - Littafi Mai Tsarki

8 Ku ma sai ku yi haƙuri, ku tsai da zukatanku, domin ranar komowar Ubangiji ta yi kusa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 Haka ku ma, ku yi haƙuri, ku tsaya da ƙarfi, gama dawowar Ubangiji ya yi kusa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Yaƙub 5:8
24 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

'Yan'uwa, kada ku yi wa juna gunaguni, don kada a hukunta ku. Ga mai shari'a a bakin ƙofa!


Albarkar Ruhu kuwa ita ce ƙauna, da farin ciki, da salama, da haƙuri, da kirki, da nagarta, da aminci,


Ka natsu a gaban Ubangiji, Ka yi haƙuri, ka jira shi, Kada ka damu da waɗanda suke da dukiya, Ko su da suka yi nasara da aikata mugayen shirye-shiryensu.


Ƙarshen dukan abubuwa ya gabato. Saboda haka, sai ku kanku, ku natsu, domin ku yi addu'a.


Bari kowa ya san jimirinku. Ubangiji ya yi kusan zuwa.


Ka dogara ga Ubangiji! Ka yi imani, kada ka karai. Ka dogara ga Ubangiji!


Shi wanda ya shaida abubuwan nan ya ce, “Hakika, ina zuwa da wuri.” Amin! Zo, ya Ubangiji Yesu.


har ya tsai da zukatanku ku zama marasa abin zargi cikin tsarki a gaban Allahnmu, Ubanmu, a ranar komowar Ubangijinmu Yesu, tare da dukan tsarkakansa.


Amma ni zan kafa ido ga Ubangiji, Zan jira ceton Allahna, Allahna zai ji ni.


Ubangiji yă tattaro hankalinku a kan ƙaunar nan ta Allah, da kuma jimirin nan na Almasihu.


In kuwa muna sa zuciya ga abin da ba mu samu ba, da jimiri mukan yi sauraronsa.


Na zaƙu, ina jiran taimako daga Ubangiji, Ga maganarsa na dogara.


ku kuma saurari komowar Ɗansa daga Sama, wanda ya tasa daga matattu, wato Yesu, mai kuɓutar da mu daga fushin nan mai zuwa.


Gama har yanzu wahayin yana jiran lokacinsa, Yana gaggautawa zuwa cikarsa, Ba zai zama ƙarya ba. Ka jira shi, ko da ka ga kamar yana jinkiri, Hakika zai zo, ba zai makara ba.


“Lokaci ya yi, ranar ta gabato, kada mai saye ya yi farin ciki, kada kuma mai sayarwa ya yi baƙin ciki, gama fushina yana kan taron jama'a duka.


Yesu ya ce masa, “In na nufe shi da wanzuwa har in zo, mene ne naka a ciki? Kai dai, bi ni!”


Su wane ne abin sa zuciyarmu, da abin farin cikinmu, da kuma abin taƙamarmu a gaban Ubangiji Yesu a ranar komowarsa, in ba ku ba?


Zinariyarku da azurfarku sun ɓāci ƙwarai, ɓācin nan nasu kuwa zai zama shaida a kanku, yă ci naman jikinku kamar wuta! Kun dai jibge dukiya a zamanin ƙarshen nan!


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ