Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Yaƙub 4:9 - Littafi Mai Tsarki

9 Ku yi nadama, ku yi baƙin ciki, ku yi ta kuka. Dariyarku tă zama baƙin ciki, murnarku tă koma ɓacin zuciya.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 Ku yi baƙin ciki, ku yi makoki ku kuma yi kuka. Ku mai da dariyarku ta zama makoki, farin cikinku kuma yă zama ɓacin zuciya.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Yaƙub 4:9
25 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Albarka tā tabbata ga masu nadāma, domin za a sanyaya musu rai.


Dariyar mutum takan ɓoye baƙin cikinsa. Sa'ad da murna ta tafi, ko yaushe baƙin ciki yana nan.


“Kaitonku, ku da kuke ƙosassu a yanzu, don za ku ji yunwa. “Kaitonku, ku masu dariya a yanzu, don za ku yi baƙin ciki, ku yi kuka.


Kafin ka hore ni nakan yi kuskure, Amma yanzu ina biyayya da maganarka.


domin ki tuna, ki gigice, ki kāsa buɗe bakinki saboda kunya, sa'ad da na gafarta miki dukan abin da kika aikata, ni Ubangiji Allah na faɗa.”


Idan akwai waɗanda suka tsere, za a same su a kan duwatsu kamar kurciyoyin kwaruruka, suna baƙin ciki dukansu, kowa yana baƙin ciki saboda laifinsa.


Amma Ibraham ya ce, ‘Ɗana, ka tuna fa, a zamanka na duniya ka sha duniyarka, Li'azaru kuwa ya sha wuya. Amma yanzu daɗi ake ba shi, kai kuwa kana shan azaba.


Saboda haka garayata ta zama ta makoki, Sarewata kuma ta zama muryar masu kuka.”


“Albarka tā tabbata gare ku, ku da kuke mayunwata a yanzu, domin za a ƙosar da kuke. “Albarka tā tabbata gare ku, ku da kuke kuka a yanzu domin za ku yi dariya.


Farin cikinmu ya ƙare, Raye-rayenmu sun zama makoki.


Sa'an nan 'yan mata za su yi rawa da farin ciki, Samari da tsofaffi za su yi murna. Zan mai da makokinsu ya zama murna, Zan ta'azantar da su, in ba su farin ciki maimakon baƙin ciki.


Da kuka za su komo. Da ta'aziyya zan bishe su, in komar da su, Zan sa su yi tafiya a gefen rafuffukan ruwa, A kan miƙaƙƙiyar hanya, inda ba za su yi tuntuɓe ba. Gama ni uba ne ga Isra'ila, Ifraimu kuwa ɗan farina ne.”


Na kuma gane dariya wauta ce, nishaɗi kuma ba shi da wani amfani.


Horon da aka yi mini ya yi kyau, Domin ya sa na koyi umarnanka.


Hawayena suna malalowa kamar kogi, Saboda jama'a ba su biyayya da shari'arka ba.


Nehemiya kuwa wanda yake mai mulki, da Ezra, firist da magatakarda, da Lawiyawa waɗanda suka fassara wa jama'a dokokin, suka ce wa dukan jama'a, “Wannan rana tsattsarka ce, ta Ubangiji Allahnku, kada ku yi baƙin ciki ko kuka.” Gama mutane duka sai kuka suke sa'ad da aka karanta musu dokokin.


Sai suka ce masa, “Zai yi wa mutanen banzan nan mugun kisa, ya ba waɗansu manoma sufurinta, waɗanda za su riƙa ba shi gallar garkar a lokacin nunanta.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ