Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Yaƙub 4:8 - Littafi Mai Tsarki

8 Ku kusaci Allah, shi ma zai kusace ku. Ku tsarkake al'amuranku, ya ku masu zunubi. Ku kuma tsarkake zukattanku, ya ku masu zuciya biyu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 Ku matso kusa da Allah shi kuwa zai matso kusa da ku. Ku wanke hannuwanku, ku masu zunubi, ku kuma tsarkake zukatanku, ku masu zuciya biyu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Yaƙub 4:8
44 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Yana kusa da dukan waɗanda suke kira gare shi, Waɗanda suke kiransa da zuciya ɗaya.


sai mu matsa kusa, da zuciya ɗaya, da cikakkiyar bangaskiya tabbatacciya, da zukatunmu tsarkakakku daga mugun lamiri, jikinmu kuma wankakke da tsattsarkan ruwa.


Ku kamar kakanninku kuke, kun bar bin dokokina, ba ku kiyaye su ba. Ku komo wurina, ni ma zan koma wurinku,” in ji Ubangiji Mai Runduna. “Amma kun ce, ‘Ƙaƙa za mu yi, mu koma gare ka?’


Domin haka sai ka ce musu, Ubangiji Mai Runduna ya ce, ‘Ku komo wurina, ni kuma zan komo wurinku, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.’


sai ya fita ya taryi Asa, ya ce masa, “Ka ji ni, ya Asa, kai da dukan Yahuza da Biliyaminu, Ubangiji yana tare da ku idan kuna tare da shi. Idan kuwa kun neme shi, za ku same shi, amma idan kun rabu da shi, shi ma zai rabu da ku.


Ya Urushalima, ki wanke mugunta daga zuciyarki, Domin a cece ki, Har yaushe mugayen tunaninki za su yi ta zama a cikinki?


Duk mai ƙwallafa sa zuciya gare shi haka, yana tsarkake kansa ke nan, kamar yadda shi yake Mai Tsarki.


Ka halitta tsarkakakkiyar zuciya a cikina, ya Allah, Ka sa sabon halin biyayya a cikina.


don Shari'a ba ta kammala kome ba, ta wani hali kuma an shigo da wani bege wanda yake mafi kyau, ta wurinsa kuwa muke kusatar Allah.


Ya ku ƙaunatattu, tun da aka yi mana waɗannan alkawarai, sai mu tsarkake kanmu daga kowace irin ƙazanta ta jiki ko ta zuci, da bangirma ga Allah mu kamalta a cikin tsarki.


Ku rabu da laifofin da kuka yi mini, sa'an nan ku samo wa kanku sabuwar zuciya da sabon hali. Don me za ku mutu, ya ku jama'ar Isra'ila?


Amma a gare ni, ya fi mini kyau, in kasance kusa da Allah! Na sami mafaka a wurin Ubangiji Allah, Da zan yi shelar dukan abin da ya aikata.


“Kai kuwa ɗana Sulemanu, sai ka san Allah na tsohonka, ka bauta masa da zuciya ɗaya, da kuma yardar rai, gama Ubangiji mai binciken dukan zukata ne, ya kuma san kowane irin nufi da tunani. Idan ka neme shi, za ka same shi, in kuwa ka rabu da shi, shi ma zai yi watsi da kai har abada.


Baftisma kuwa, wadda ita ce kwatancin wannan, ta cece ku a yanzu, ba ta fitar da dauɗa daga jiki ba, sai dai ta wurin roƙon Allah da lamiri mai kyau, ta wurin tashin Yesu Almasihu daga matattu,


Har su ma da suke cewa su mutanen kirki ne Suna ƙara tabbatarwa ba su yi kuskure ba.


“Ko dai ku ce itace kyakkyawa ne, 'ya'yansa kuma kyawawa, ko kuwa ku ce itace mummuna ne, 'ya'yansa kuma munana. Don itace, da 'ya'yansa ake gane shi.


Saboda haka, a kowane wuri ina so maza su yi addu'a, suna ɗaga hannuwa tsarkakakku, ba tare da fushi ko jayayya ba.


Ubangiji ya ce, “Waɗannan mutane sun ce suna mini sujada, amma kalmominsu ba su da ma'ana, zukatansu kuma suna wani wuri dabam. Addininsu ba wani abu ba ne, sai dai dokoki ne da ka'idodin mutane da suka haddace.


Sai wanda yake da tsarki cikin aiki, da tunani, Wanda ba ya yi wa gumaka sujada, Ko kuma yă yi alkawarin ƙarya.


Da yake kun tsarkake ranku kuna yi wa gaskiya biyayya har kuna nuna sahihiyar ƙauna ga 'yan'uwa, sai ku himmantu ga ƙaunar juna da zuciya ɗaya.


Ubangiji yakan sāka mini, saboda ni adali ne, Yakan sa mini albarka, don ni marar laifi ne.


Ya Ubangiji, na wanke hannuwana Don in nuna ba ni da laifi, Da ibada nakan taka, ina kewaya bagadenka.


Bai kuma nuna wani bambanci tsakaninmu da su ba, tun da yake ya tsarkake zukatansu saboda bangaskiyarsu.


Sai Ibrahim ya matso kusa, ya ce, “Ashe, za ka hallaka adali tare da mugun?


Amma ban yi wani aikin kama-karya ba, Addu'ata ga Allah kuwa ta gaskiya ce.


“Don me almajiranka suke keta al'adun shugabanni? Domin ba sa wanke hannu kafin su ci abinci.”


Lokaci yana zuwa da za a faɗa wa mutanen Urushalima cewa, “Iska mai zafi za ta huro daga tuddan hamada zuwa wajen jama'ata, ba domin a sheƙe ta ko a rairaye ta ba!


Ashe, a banza nake kiyaye kaina da tsarki, Hannuwana kuma a tsabtace daga zunubi?


Da Bilatus ya ga bai rinjaye su ba, sai dai hargitsi yana shirin tashi, sai ya ɗibi ruwa ya wanke hannunsa a gaban jama'a, ya ce, “Ni kam, na kuɓuta daga alhakin jinin mai adalcin nan. Wannan ruwanku ne.”


Saul kuwa ya gina wa Ubangiji bagade. Shi ne bagade na farko da ya gina wa Ubangiji.


Ina ƙin waɗanda ba su yi maka aminci, Amma ina ƙaunar dokarka.


Duk da haka suna ta nemana kowace rana, suna murna su san al'amurana, sai ka ce su al'umma ce wadda take aikata adalci, wadda kuma ba ta rabu da dokokin Allahnta ba. Suna roƙona in yi musu shari'ar adalci, suna murna su zo kusa da Allah.”


Amma hikimar nan ta Sama, da farko dai tsattsarka ce, mai lumana ce, saliha ce, mai sauƙin kai, mai tsananin jinƙai, mai yawan alheri, mai kaifi ɗaya, sahihiya kuma.


Sa'ad da na yi kira gare ka, ka zo kusa. Sa'an nan ka ce mini kada in ji tsoro.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ