Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Yaƙub 4:10 - Littafi Mai Tsarki

10 Ku ƙasƙantar da kanku ga Ubangiji, shi kuwa zai ɗaukaka ku.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

10 Ku ƙasƙantar da kanku a gaban Ubangiji, zai kuwa ɗaukaka ku.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Yaƙub 4:10
19 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Yakan ɗaukaka masu tawali'u, Amma yakan ragargaza mugaye har ƙasa.


Duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Mai ƙasƙantar da kansa kuma, ɗaukaka shi za a yi.


Don haka, sai dai ku ƙasƙantar da kanku ga maɗaukakin ikon Allah, domin ya ɗaukakaku a kan kari.


Duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Mai ƙasƙantar da kansa kuma, ɗaukaka shi za a yi.”


Allah yakan ƙasƙantar da mai girmankai, Yakan ceci mai tawali'u.


Yakan ɗaga talakawa daga ƙura, Yakan ɗaga matalauta daga cikin azabarsu.


Ya firfitar da sarakuna a sarauta, Ya ɗaukaka ƙasƙantattu.


Ina dai gaya muku, wannan mutum ya koma gidansa baratacce, ba kamar ɗayan ba. Don duk mai ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Mai ƙasƙantar da kansa kuwa, ɗaukaka shi za a yi.”


Ta haka zan ci nasara a kan magabtana da suke kewaye da ni. Da sowar farin ciki mai yawa zan miƙa sadakoki a Haikalinsa! Zan raira waƙa, in yabi Ubangiji!


Ina yabonka, ya Ubangiji saboda ka cece ni, Ka kuwa hana magabtana su haɗiye ni.


“Zai kiyaye rayukan amintattun mutanensa, Amma mugayen mutane za su lalace cikin duhu, Ba ƙarfin mutum yake sa ya yi nasara ba.


Ka ceci jama'arka, ya Ubangiji, Ka sa wa waɗanda suke naka albarka! Ka zama makiyayinsu, Ka lura da su har abada.


Saboda haka Musa da Haruna suka tafi gaban Fir'auna suka ce masa, “Ga abin da Ubangiji Allah na Ibraniyawa ya ce, ‘Har yaushe za ka ƙi yarda ka ba da kanka a gare ni? Saki jama'ata don su tafi su yi mini sujada.


Yakan sa waɗansu mutane su zama matalauta, Waɗansu kuwa attajirai. Yakan ƙasƙantar da waɗansu, Ya kuma ɗaukaka waɗansu.


in jama'ata waɗanda ake kiransu da sunana za su yi tawali'u, su yi addu'a, su nemi fuskata, su juyo su bar mugayen ayyukansu, sa'an nan sai in ji su daga Sama, in gafarta zunubansu, in kuma warkar da ƙasarsu.


I, Allah ne yake ɗaukaka masu tawali'u, Shi yake kuɓutar da dukan waɗanda suke makoki.


Girmankan mutum zai jawo masa ƙasƙanci, amma za a girmama mai tawali'u.


Ni Ubangiji Allah na ce, ka cire rawaninka, ka ɗauke kambinka. Abubuwa ba za su kasance kamar yadda suke a dā ba. Za a ɗaukaka ƙasƙantacce, amma a ƙasƙantar da maigirma.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ