Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Yaƙub 1:26 - Littafi Mai Tsarki

26 In wani yana zaton shi mai addini ne, amma bai kame bakinsa ba, sai dai ya yaudari kansa, to, addinin mutumin nan na banza ne.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

26 In wani ya ɗauki kansa mai addini ne duk da haka bai ƙame harshensa ba, ruɗin kansa yake yi addininsa kuwa banza ne.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Yaƙub 1:26
37 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Kada wata alfasha ta fita daga bakinku, sai dai irin maganar da ta kyautu domin ingantawa, a kuma yi ta a kan kari, domin ta sa alheri ga masu jinta.


Ya Ubangiji, ka sa a yi tsaron bakina, Ka sa mai tsaro a leɓunana.


Domin, “Duk mai so ya more wa zamansa na duniya da alheri, Sai ya kame bakinsa daga ɓarna, Ya kuma hana shi maganar yaudara.


Haka ma alfasha, da zancen banza da wauta, don bai kamata ba, sai dai a maimakon haka ku riƙa gode wa Allah.


Gara mutum ya zama matalauci amma mai aminci, da a ce ya zama maƙaryaci, wawa.


To, ku yi nisa da mugun baki, Da faɗar ƙarairayi.


Maganar adalai ta hikima ce, amma harshen da yake hurta mugunta, za a dakatar da shi.


Bisa ga yawan surutunka, mai yiwuwa ne ƙwarai ka yi zunubi, amma idan kai mai la'akari ne, sai ka yi shiru.


A kullum maganarku ta zama mai ƙayatarwa, mai daɗin ji, domin ku san irin amsar da ta dace ku ba kowa.


Amma ku zama masu aikata maganar, ba masu ji kawai, kuna yaudarar kanku ba.


Ya 'yan'uwana ƙaunatattu, ku san wannan, wato, kowa yă yi hanzarin kasa kunne, da jinkirin yin magana, da kuma jinkirin yin fushi,


Hanyar da kake tsammani ita ce daidai, za ta kai ka ga hallaka.


Ku kula fa, ku iya ji, don mai abu akan ƙara wa. Marar abu kuwa, ko ɗan abin da yake tsammani yake da shi ma, sai a karɓe masa.”


Kowa ya zaci shi wani abu ne, alhali kuwa shi ba kome ba ne, ya ruɗi kansa ke nan.


Hanyar da kake tsammani ita ce daidai, za ta kai ka ga hallaka.


Ku lura fa, kada zuciya ta ruɗe ku, har ku kauce, ku bauta wa waɗansu alloli, ku yi musu sujada,


Waɗanda kuma aka ɗauka a dā a kan su wani abu ne (ko su wane ne, ai, duk ɗaya ne a guna, domin Allah ba ya tāra), ina dai gaya muku waɗannan da suke wani abu ne a dā, ba su ƙare ni da kome ba.


A banza suke bauta mini, Domin ƙa'idodin da suke koyarwa umarnin ɗan adam ne.’


Ya zama daidai kamar mutum ya ci toka. Manufarsa ta wauta ta ɓatar da shi, har ba yadda za a iya taimakonsa. Ba zai iya ganewa ba, gunkin da ya riƙe a hannunsa ba allah ba ne ko kaɗan.


Duk abin da yake tunani dukan yini, shi ne a kan abin da yake so ya samu. Amma adali ko ta ƙaƙa yakan bayar da hannu sake.


wadda kuma ake cetonku da ita, muddin kun riƙe maganar da na sanar da ku da kyau, in ba sama sama ne kuka gaskata ba.


A banza suke bauta mini, Don ka'idodin da suke koyarwa umarnin ɗan adam ne.’ ”


Kun ce, ‘Ba amfani a bauta wa Ubangiji. Ina amfani a kiyaye abin da ya ce, ko mu yi ƙoƙarin nuna cewa zuciyarmu ta ɓāci saboda ayyukan da muka yi wa Ubangiji Mai Runduna.


Ko kusa ba na bukatar hadayunku marasa amfani. Ina jin ƙyamar ƙanshin turaren da kuke miƙawa. Ba zan jure da bukukuwanku na amaryar wata, da na ranakun Asabar, da taronku na addini ba, duka sun ɓaci saboda zunubanku.


Sai ma ya zamana mun yi wa Allah shaidar zur ke nan, domin mun shaida Allah, cewa ya ta da Almasihu, wanda kuwa bai tasar ba, in da gaskiya ne ba a ta da matattu.


Sarkin da yakan yi magana ta wurin ikon Allah, a ko yaushe yakan yanke shawarar da yake daidai.


Sa'ad da mai hikima ya yi magana yakan sa ilimi ya yi bansha'awa, amma wawaye sukan yi ta sheƙa rashin hankali.


Kada ka zama wawa kamar doki ko alfadari, Wanda dole sai da linzami, da ragama za a sarrafa shi, Sa'an nan yă yi maka biyayya.”


Kai marar azanci! Wato sai an nuna maka, bangaskiya ba tare da aikatawa ba, wofiya ce?


Ashe, a banza kuka sha wuya iri iri? In dai har a banzan ne!


sai Yakubu da Kefas da Yahaya, su da suke shahararrun ginshiƙan ikkilisiya, da suka ga alherin da Allah ya yi mini, sai suka karɓe mu, ni da Barnaba, hannu biyu biyu, domin mu mu je wurin al'ummai, su kuwa gun masu kaciya.


Kada kowa yă ruɗi kansa. In waninku ya zaci shi mai hikima ne, yadda duniya ta ɗauki hikima, sai yă mai da kansa marar hikima, domin ya sami zama mai hikima.


Domin Allah ya katse lakata, ya ƙasƙanta ni, Saboda haka sun raba ni da zuriyata,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ