Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Yahuda 1:8 - Littafi Mai Tsarki

8 Haka kuma masu mafarke-mafarken nan, sukan ƙazantar da jikinsu, su ƙi bin mulki, su kuma yi wa masu ɗaukaka baƙar magana.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 Haka yake da masu mafarke-mafarken nan, gama sun ƙazantar da jikunansu, suka ƙi bin masu mulki, suna ɓata sunan talikan sararin sama.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Yahuda 1:8
23 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ku yi wa shugabanninku biyayya, ku bi umarnansu, don su ne masu kula da rayukanku, su ne kuma za su yi lissafin aikinsu, don su yi haka da farin ciki, ba da baƙin ciki ba, don in sun yi da baƙin ciki ba zai amfane ku ba.


Ku girmama kowa, ku ƙaunaci 'yan'uwa, ku ji tsoron Allah, ku girmama sarki.


da fasikai, da masu luɗu, da masu sace mutane, da maƙaryata, da masu shaidar zur, da kuma duk sauran abin da ya sāɓa sahihiyar koyarwar nan,


Sai Bulus ya ce, “Ai, ban sani shi ne babban firist ba, 'yan'uwa, don a rubuce yake cewa, ‘Kada ka munana shugaban jama'a.’ ”


Kada ka zagi sarki ko a cikin zuciyarka, kada kuma ka zagi mawadaci a cikin ɗakin kwananka, gama tsuntsu zai kai maganarka, wani taliki mai fikafikai zai tone asirinka.


“Kada ku saɓi Allah, kada kuma ku zagi mai mulkin jama'arku.


In wani ya ɓāta Haikalin Allah, Allah zai ɓāta shi. Gama Haikalin Allah tsattsarka ne, ku kanku Haikalinsa ne.


Saboda haka, kowa ya ƙi yarda da wannan, ba mutum ya ƙi ba, amma Allah ya ƙi, shi da yake ba ku Ruhunsa Mai Tsarki.


Amma kakanninmu suka ƙi yi masa biyayya, suka ture shi, zuciya tasu ta koma ƙasar Masar.


Amma mai cutar ɗan'uwa nasa ya ture Musa, ya ce, ‘Wa ya sa ka shugaba da alƙali a kanmu?


Amma mutanensa suka ƙi shi, har suka aiki jakadu a bayansa, cewa ba sa so ya yi mulki a kansu.


Idan ɗa ya raina mahaifi, ya kuma yi wa mahaifiya ba'a hankakin kwari za su ƙwaƙule masa idanu, 'ya'yan mikiya za su cinye.


Akwai waɗansu mutane da sukan zagi iyayensu maza, ba sukan kuma nuna godiya ga iyayensu mata ba.


Suka taru a gaban Musa da Haruna, suka ce musu, “Kun cika izgili, gama dukan taron jama'a na Ubangiji ne, Ubangiji kuwa yana tare da su. Me ya sa kai Musa ka aza kanka shugaba a kan taron jama'ar Ubangiji?”


Gama Allah ya sani a ranar da kuka ci daga itacen nan idanunku za su buɗe, za ku kuwa zama kamar Allah, ku san nagarta da mugunta.”


Sa'ad da suka kai ku gaban majami'u, da mahukunta da shugabanni, kada ku damu da yadda za ku mai da jawabi, ko kuwa abin da za ku faɗa,


Sa'ad da kuwa ya komo gidan ya tarar da shi shararre, ƙawatacce,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ