Mutumin da ba shi da Ruhu yakan ƙi yin na'am da al'amuran Ruhun Allah, don wauta ne a gare shi, ba kuwa zai iya fahimtarsu ba, domin ta wurin ruhu ne ake rarrabewa da su.
Amma ku kam, ba masu zaman halin mutuntaka ba ne, masu zaman Ruhu ne, in dai har Ruhun Allah yana zaune a zuciyarku. Duk wanda ba shi da Ruhun Almasihu kuwa, ba na Almasihu ba ne.
Ubangiji ya ce, “Na iske Isra'ila a jeji kamar inabi, Na ga kakanninku kamar nunan fari na 'ya'yan ɓaure, Amma da suka zo Ba'al-feyor, sai suka keɓe kansu ga Ba'al. Suka zama abin ƙyama kamar abin da suke ƙauna.
Ba zan hukunta 'ya'yanku mata sa'ad da suka yi karuwanci ba, Ko kuwa surukanku mata sa'ad da suka yi zina ba, Gama mazan da kansu sukan shiga wurin karuwai. Sukan miƙa sadaka tare da karuwai a Haikali, Mutane marasa fahimi za su lalace.
“‘Gama duk wanda yake na Isra'ila da dukan baƙin da suke baƙunta cikin Isra'ila, wanda ya rabu da ni, ya manne wa gumakansa, ya sa abin tuntuɓe a gabansa, sa'an nan ya zo yana roƙona a wurin annabi, ni Ubangiji zan sāka masa.
Sa'an nan su riƙa ce wa sauran mutane, ‘Ku yi nesa da mu gama muna da tsarki da yawa, har da ba za mu taɓa ku ba.’ Ba zan daure da irin waɗannan mutane ba, fushina a kansu kamar wuta ce wadda ba za ta taɓa mutuwa ba.