Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Yahuda 1:17 - Littafi Mai Tsarki

17 Ya ku ƙaunatattuna, lalle ku tuna da maganar da manzannin Ubangijinmu Yesu Almasihu suka faɗa a dā,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

17 Amma ku abokaina ƙaunatattu, ku tuna da abin da manzannin Ubangijinmu Yesu Kiristi suka faɗa a dā.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Yahuda 1:17
8 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ina so ku tuna da yin faɗin annabawa tsarkaka, da kuma umarnin Ubangiji Mai Ceto ta bakin manzannin da suka zo muku.


Mu kam na Allah ne. Duk wanda ya san Allah yakan saurare mu, wanda yake ba na Allah ba kuwa, ba ya sauraronmu. Ta haka muka san Ruhu na gaskiya da ruhu na ƙarya.


Ya kuma yi wa waɗansu baiwa su zama manzanni, waɗansu annabawa, waɗansu masu yin bishara, waɗansu makiyaya masu koyarwa,


Na zamar muku abin misali ta kowace hanya, cewa ta wahalar aiki haka lalle ne a taimaki masu ƙaramin ƙarfi, kuna kuma tunawa da Maganar Ubangiji Yesu da ya ce, ‘Bayarwa ta fi karɓa albarka.’ ”


“Ku tuna da koyarwar bawana Musa, da dokoki, da umarnai waɗanda na ba shi a kan Dutsen Horeb, domin dukan jama'ar Isra'ila su kiyaye.


waɗanda aka gina bisa tushen manzanni da annabawa, Almasihu Yesu kansa kuwa shi ne mafificin dutsen ginin,


to, ta ƙaƙa mu za mu tsira, in mun ƙi kula da ceto mai girma haka? Domin Ubangiji kansa, shi ne ya fara sanar da shi, waɗanda suka saurare shi kuma suka tabbatar mana da shi,


Ya ku ƙaunatattuna, da yake dā ma ina ɗokin rubuto muku zancen ceton nan namu, mu duka, sai na ga wajibi ne in rubuto muku in gargaɗe ku, ku dage ƙwarai a kan bangaskiyar nan da aka danƙa wa tsarkaka sau ɗaya tak, ba ƙari.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ