Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




W.Yah 9:18 - Littafi Mai Tsarki

18 Da waɗannan bala'i uku aka kashe sulusin 'yan adam, wato, da wuta, da hayaƙi, da farar wuta da suke fita daga bakinsu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

18 Aka kashe kashi ɗaya bisa uku na ’yan Adam da annobai uku na wuta, hayaƙi da farar wuta da suka fito daga bakunansu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




W.Yah 9:18
9 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ga kuwa yadda na ga dawakan a wahayin da aka yi mini, mahayansu suna saye da sulkuna, launinsu ja kamar wuta, da shuɗi, da kuma rawaya kamar farar wuta, kawunan dawakan kuma kamar na zaki, wuta kuma da hayaƙi da farar wuta suna fita daga bakinsu.


Sai aka saki mala'ikun nan huɗu, waɗanda aka tanada saboda wannan sa'a, da wannan rana, da wannan wata, da wannan shekara, su kashe sulusin 'yan adam.


Mala'ikan farko ya busa ƙahonsa, sai ga ƙanƙara da wuta, gauraye da jini. Aka zuba su a duniya, sai sulusin duniya ya ƙone, sulusin itatuwa suka ƙone, dukkan ɗanyar ciyawa kuma ta ƙone.


Mala'ika na biyu ya busa ƙahonsa, sai aka jefa wani abu a teku kamar babban dutse mai tsawo, mai cin wuta. Sulusin teku ya zama jini,


sulusin halittar da suke a ruwa suka mutu, sulusin jiragen ruwa kuma suka hallaka.


Mala'ika na uku ya busa ƙahonsa, sai wani babban tauraro ya faɗo daga sama, yana cin wuta kamar cukwima. Ya faɗa a sulusin koguna da maɓuɓɓugan ruwa.


Sunan tauraron kuwa Ɗaci. Sulusin ruwa ya zama mai ɗaci, sai mutane da yawa suka mutu saboda shan ruwan, don ɗacinsa.


Mala'ika na huɗu ya busa ƙahonsa, sai aka bugi sulusin rana, da sulusin wata, da kuma sulusin taurari, har sulusin haskensu ya zama duhu, wato ba haske a sulusin yini, haka kuma a sulusin dare.


Domin ikon dawakan nan na a bakinsu da a wutsiyarsu, wutsiyoyinsu kamar macizai suke, har da kawuna, da su ne suke azabtarwa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ