W.Yah 9:17 - Littafi Mai Tsarki17 Ga kuwa yadda na ga dawakan a wahayin da aka yi mini, mahayansu suna saye da sulkuna, launinsu ja kamar wuta, da shuɗi, da kuma rawaya kamar farar wuta, kawunan dawakan kuma kamar na zaki, wuta kuma da hayaƙi da farar wuta suna fita daga bakinsu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202017 Dawakai da masu hawansu da na gani cikin wahayina sun yi kamar. Sulkunansu ja wur ne, baƙin shuɗi, da kuma rawaya kamar farar wuta. Kawunan dawakan sun yi kamar kawunan zakoki, daga bakunansu kuwa wuta, hayaƙi, da farar wuta suna fitowa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |