Kogin wuta yana gudu daga gabansa. Dubun dubbai suna ta yi masa hidima, Dubu goma sau dubu goma suka tsaya a gabansa, Aka kafa shari'a, aka buɗe littattafai.
Zan juyar da kai, in sa ƙugiyoyi cikin muƙamuƙanka, in fitar da kai, da dukan sojojinka, da dawakai da mahayansu. Su babbar runduna ce saye da makamai, wato garkuwoyi, da takuba a zāre,
Sa'an nan na duba, sai na ji muryar mala'iku masu yawa, a kewaye da kursiyin, da rayayyun halittan nan, da kuma dattawan nan, yawansu zambar dubu har dubun dubbai,
“A lokaci na ƙarshe sarkin kudu zai tasar masa, sarkin arewa kuwa zai tunzura, ya tasar masa da karusai da mahayan dawakai, da jiragen ruwa da yawa. Zai ratsa ƙasashe, ya ci su da yaƙi, ya wuce.