W.Yah 7:3 - Littafi Mai Tsarki3 yana cewa, “Kada ku azabtar da ƙasa, ko teku, ko itatuwa, sai mun buga wa bayin Allahnmu hatimi a goshinsu tukuna.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20203 “Kada ku cuci ƙasa ko teku ko kuma itatuwa sai bayan mun sa hatimi a goshin dukan bayin Allahnmu.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa'an nan na ga kursiyai, da waɗanda aka bai wa ikon hukunci, zaune a kai. Har wa yau, kuma na ga rayukan waɗanda aka fille wa kai saboda shaidar da suka yi wa Yesu, da kuma Maganar Allah, ba su kuwa yi wa dabbar nan da siffarta sujada ba, ba su kuma yarda a yi musu alamarta a goshinsu ko a hannunsu ba, sun sāke rayuwa, sun yi mulki tare da Almasihu har shekara dubu.