Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




W.Yah 5:8 - Littafi Mai Tsarki

8 Da ya ɗauki littafin, rayayyun halittan nan guda huɗu, da dattawan nan ashirin da huɗu, suka fāɗi gaban Ɗan Ragon, kowannensu yana riƙe da molo, da tasar zinariya a cike da turare, waɗanda suke addu'o'in tsarkaka.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 Bayan ya karɓa, sai halittu huɗun nan masu rai da kuma dattawan nan ashirin da huɗu suka fāɗi ƙasa a gaban Ɗan Ragon. Kowannensu yana da garaya kuma suna riƙe da kaskon zinariya cike da turare, waɗanda suke addu’o’in tsarkaka.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




W.Yah 5:8
27 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ka karɓi addu'ata kamar turaren ƙonawa, Ka karɓi ɗaga hannuwa sama da na yi kamar hadayar maraice.


sai dattawan nan ashirin da huɗu suka fāɗi a gaban wanda yake a zaune a kan kursiyin, su yi masa sujada, shi da yake a raye har abada abadin, su kuma ajiye kambinsu a gaban kursiyin, suna waƙa, suna cewa,


Sai rayayyun halittan nan huɗu suka ce, “Amin! Amin!” Dattawan nan kuma suka fāɗi suka yi sujada.


Kewaye da kursiyin kuwa akwai waɗansu kursiyai ashirin da huɗu, da dattawa ashirin da huɗu a zaune a kai, masu fararen tufafi, da kuma kambin zinariya a kansu.


Sai dattawan nan ashirin da huɗu, da rayayyun halittan nan huɗu, suka fāɗi suka yi wa Allah sujada, shi da yake zaune a kan kursiyin, suna cewa, “Amin. Halleluya!”


Sai na ga wani Ɗan Rago yana a tsaye a tsakiyar kursiyin, kewaye da shi kuma ga rayayyun halittan nan huɗu da dattawan, Ɗan Ragon kuwa kamar yankakke ne, yana da ƙaho bakwai da ido bakwai, waɗanda suke Ruhohin Allah guda bakwai, da aka aika a duniya duka.


Su rayayyun halittan nan huɗu kuwa, kowaccensu tana da fikafikai shida, jikinsu duk idanu ne ciki da waje, dare da rana kuwa ba sa daina waƙa, suna cewa, “Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki, Ubangiji Allah Maɗaukaki, Shi ne a dā, shi ne a yanzu, shi ne kuma a nan gaba!”


Ku kaɗa garaya, kuna yi wa Ubangiji godiya. Ku raira masa waƙa, da kayan kaɗe-kaɗe masu tsarkiya.


Sai ɗaya daga cikin rayayyun halittan nan guda huɗu, ta ba mala'ikun nan bakwai tasoshi bakwai na zinariya, a cike da fushin Allah, shi da yake a raye har abada abadin.


Sai na ga wani abu kamar bahar na gilas, gauraye da wuta, na kuma ga waɗanda suka yi nasara da dabbar nan, da siffarta, da kuma lambar sunanta, a tsaitsaye a bakin bahar na gilas, da molayen yabon Allah a hannunsu.


domin kowa yă girmama Ɗan, kamar yadda ake girmama Uban. Wanda ba ya girmama Ɗan, ba ya girmama Uban da ya aiko shi ke nan.


A fara waƙa, ku buga bandiri, Ku yi waƙoƙi masu daɗi da molaye, da garayu.


Sa'an nan zan tafi wurin bagadenka, ya Allah, Zuwa gare ka, kai wanda kake sa ni in yi murna da farin ciki, In raira waƙar yabo a gare ka da garayata, Ya Allah, Allahna!


Ku yabe shi da kakaki! Ku yabe shi da garayu da molaye!


Amma da zai sāke shigo da magāji a duniya, sai ya ce, “Dukkan mala'ikun Allah su yi masa sujada.”


Kashegari Yahaya ya tsinkayo Yesu na nufo shi, sai ya ce, “Kun ga, ga Ɗan Rago na Allah, wanda zai ɗauke zunubin duniya!


A gaban kursiyin kuwa akwai wani abu kamar bahar na gilas, garau yake kamar ƙarau. Kewaye da kursiyin kuma, ta kowane gefensa, da waɗansu rayayyun halitta guda huɗu, masu idanu ta ko'ina, gaba da baya.


Sa'an nan na duba, sai na ji muryar mala'iku masu yawa, a kewaye da kursiyin, da rayayyun halittan nan, da kuma dattawan nan, yawansu zambar dubu har dubun dubbai,


suna cewa da murya mai ƙarfi, “Macancanci ne Ɗan Ragon nan da aka yanka yă sami iko, da wadata, da hikima, da ƙarfi, da girma, da ɗaukaka, da yabo!”


To, ina gani sa'ad da Ɗan Ragon nan ya ɓamɓare ɗaya daga cikin hatiman nan bakwai, na ji ɗaya daga cikin rayayyun halittan nan huɗu ta yi magana kamar aradu ta ce, “Zo.”


Duk mazaunan duniya kuma, za su yi mata sujada, wato, duk wanda, tun farkon duniya, ba a rubuta sunansa a Littafin Rai na Ɗan Ragon nan da yake Yankakke ba.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ