Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




W.Yah 5:5 - Littafi Mai Tsarki

5 Sai ɗaya daga cikin dattawan nan ya ce mini, “Kada ka yi kuka. Ga shi, Zakin nan na kabilar Yahuza, Tsatson Dawuda, ya ci nasara har yake da iko yă buɗe littafin nan da hatimansa bakwai.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 Sai ɗaya daga cikin dattawan ya ce mini, “Kada ka yi kuka! Duba, Zakin kabilar Yahuda, da kuma Tushen Dawuda ya ci nasara. Ya iya buɗe naɗaɗɗen littafin da hatimansa bakwai.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




W.Yah 5:5
25 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Gidan sarautar Dawuda kamar itacen da aka sare ne, amma kamar yadda rassa sukan toho daga cikin kututture, haka nan za a sami sabon sarki daga zuriyar Dawuda.


“Ni Yesu, na aiko mala'ikana a gare ka, da wannan shaida saboda ikilisiyoyi. Ni ne tsatson Dawuda, da zuriyarsa, Gamzaki mai haske.”


Tabbatacce ne, cewa Ubangijinmu ya fito daga zuriyar Yahuza ne, Musa kuwa bai ce kome ba a game da kabilar nan a kan zancen firistoci.


Ishaya kuma ya ce, “Tsatson Yesse zai bayyana, Wanda zai tashi yă mallaki al'ummai, A gare shi ne al'ummai za su sa zuciya.”


Bishara ɗin nan a kan Ɗansa ce, Ubangijinmu Yesu Almasihu, wanda ga jiki shi zuriyar Dawuda ne,


Rana tana zuwa sa'ad da sabon sarki zai fito daga cikin gidan sarautar Dawuda, zai zama alama ga sauran al'umma. Za su tattaru a birnin sarautarsa su girmama shi.


To, ina gani sa'ad da Ɗan Ragon nan ya ɓamɓare ɗaya daga cikin hatiman nan bakwai, na ji ɗaya daga cikin rayayyun halittan nan huɗu ta yi magana kamar aradu ta ce, “Zo.”


Kewaye da kursiyin kuwa akwai waɗansu kursiyai ashirin da huɗu, da dattawa ashirin da huɗu a zaune a kai, masu fararen tufafi, da kuma kambin zinariya a kansu.


Ki yi shiru, ki daina kuka, Ki shafe hawaye daga idanunki. Za a sāka miki wahalarki, Za su komo daga ƙasar abokin gāba, Ni Ubangiji na faɗa.


Sai ɗaya daga cikin dattawan nan ya yi mini magana, ya ce, “Su wane ne waɗannan da suke a saye da fararen riguna, daga ina kuma suke?”


sai dattawan nan ashirin da huɗu suka fāɗi a gaban wanda yake a zaune a kan kursiyin, su yi masa sujada, shi da yake a raye har abada abadin, su kuma ajiye kambinsu a gaban kursiyin, suna waƙa, suna cewa,


Wahayin Yesu Almasihu da Allah ya ba shi ya nuna wa bayinsa abin da lalle ne zai auku ba da daɗewa ba, ya kuwa bayyana shi ta wurin aiko da mala'ikansa zuwa gun bawansa Yahaya,


Suka ce mata, “Uwargida, don me kike kuka?” Ta ce musu, “Ai, an ɗauke Ubangijina, ban kuwa san inda aka sa shi ba.”


Da Ubangiji ya gan ta, ya ji tausayinta, ya kuma ce mata, “Daina kuka.”


Al'ummar tana kama da ƙaƙƙarfan zaki Sa'ad da yake barci, ba wanda zai yi ƙarfin hali ya tashe shi. Duk wanda ya sa muku albarka zai sami albarka, Duk wanda ya sa muku la'ana zai sami la'ana.”


Amma Yesu ya juya gare su, ya ce, “Ya ku matan Urushalima, ku bar yi mini kuka, sai dai ku yi wa kanku da kuma 'ya'yanku,


Duk kuwa ana ta kuka da kururuwa saboda ita. Amma Yesu ya ce, “Ku daina kuka. Ai, ba matacciya take ba, barci take yi.”


Sai na matsa kusa da ɗaya daga cikin waɗanda suke tsaye a wurin, na tambaye shi ma'anar waɗannan abubuwa duka. Sai ya bayyana mini, ya kuma ganar da ni ma'anar waɗannan abubuwa.


Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi izinin zama tare da ni a kursiyina. kamar yadda ni ma na ci nasara, na kuma zauna tare da Ubana a kursiyinsa.


Sai na yi ta kuka da ba a sami wanda ya cancanta ya buɗe littafin, ko ya duba a cikinsa ba, ko ɗaya.


Akwai siffar zaki goma sha biyu suna tsaye a kowane gefen matakan nan shida. Ba a taɓa yin irinsu a kowace masarauta ba.


Gadon sarautar yana da matakai da 'yar kujerar zinariya ta ɗora ƙafa haɗe da gadon. A kowane gefen gadon an yi wurin ɗora hannu, akwai kuma siffar zaki a tsaye kusa da kowane wurin ɗora hannun.


An yi gadon bayansa da jerin garkuwoyi ne, An haɗa su daɓa-daɓa kamar an liƙe.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ