W.Yah 4:4 - Littafi Mai Tsarki4 Kewaye da kursiyin kuwa akwai waɗansu kursiyai ashirin da huɗu, da dattawa ashirin da huɗu a zaune a kai, masu fararen tufafi, da kuma kambin zinariya a kansu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20204 Kewaye da kursiyin kuwa akwai waɗansu kursiyoyi ashirin da huɗu, zaune a kansu kuwa dattawa ashirin da huɗu ne. Suna saye da fararen tufafi suna kuma da rawanin zinariya a kawunansu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa'an nan na ga kursiyai, da waɗanda aka bai wa ikon hukunci, zaune a kai. Har wa yau, kuma na ga rayukan waɗanda aka fille wa kai saboda shaidar da suka yi wa Yesu, da kuma Maganar Allah, ba su kuwa yi wa dabbar nan da siffarta sujada ba, ba su kuma yarda a yi musu alamarta a goshinsu ko a hannunsu ba, sun sāke rayuwa, sun yi mulki tare da Almasihu har shekara dubu.