Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




W.Yah 4:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Na zaunen kuwa ya yi kama da yasfa da yakutu. Kewaye da kursiyin kuma akwai wani bakan gizo mai kama da zumurrudu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Wannan mai zama a can kuwa yana da kamannin dutsen yasfa da karneliya. Bakan gizo, mai kama da zumurrudu, ya kewaye kursiyin.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




W.Yah 4:3
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Kamar kamannin bakan gizo a cikin gizagizai a ranar da aka yi ruwan sama, haka nan kamannin hasken da yake kewaye da shi yake. Wannan shi ne kamannin kwatancin ɗaukakar Ubangiji. Sa'ad da na gani, sai na faɗi rubda ciki, na ji muryar wani tana magana.


yana tare da ɗaukakar Allah. Hasken birnin yana ƙyalƙyali kamar wani irin nadirin dutse mai daraja, kamar yasfa, garau kamar ƙarau.


Sa'an nan na ga wani ƙaƙƙarfan mala'ika yana saukowa daga sama, lulluɓe da gajimare, da bakan gizo a bisa kansa, fuskarsa kamar rana, ƙafafunsa kuma kamar ginshiƙan wuta.


Kana cikin Aidan, gonar Allah. An yi maka sutura da kowane irin dutse mai daraja, Tare da zinariya. Kana da molo da abin busa. A ranar da aka halicce ka Suna nan cikakku.


A saman al'arshin akwai wani abu mai kamar kursiyin sarauta da aka yi da yakutu. Akwai wani kamar mutum yana zaune a kan abin nan mai kama da kursiyin sarauta.


Suka ga Allah na Isra'ila. Wurin da yake ƙarƙashin tafin ƙafafunsa yana kama da daɓen da aka yi da dutsen yakutu, garau kamar sararin sama.


A jeri na biyu aka sa turkos, da saffir, da daimon.


A jeri na biyu, a sa turkos, da saffir, da daimon.


A shekarar da sarki Azariya ya rasu na ga Ubangiji. Yana zaune a kursiyinsa a Sama cike da ɗaukaka, zatinsa ya cika Haikali.


Da na duba sararin sama da yake bisa kawunan kerubobi, sai na ga wani abu ya bayyana kamar yakutu. Fasalinsa kamar na kursiyi.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ