W.Yah 3:7 - Littafi Mai Tsarki7 “Ka kuma rubuta wa mala'ikan ikkilisiyar da take a Filadalfiya haka, ‘Ga maganar Mai Tsarkin nan, Mai gaskiya, wanda yake da mabuɗin Dawuda, wanda in ya buɗe, ba mai rufewa, in kuma ya rufe, ba mai buɗewa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20207 “Zuwa ga mala’ikan ikkilisiya a Filadelfiya, ka rubuta, Waɗannan su ne kalmomi, na wanda yake mai tsarki da kuma gaskiya, wanda yake riƙe da mabuɗin Dawuda. Abin da ya buɗe ba mai rufewa, abin da kuma ya rufe ba mai buɗewa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Allah Mai Tsarki na Isra'ila, Mai Fansa, Ya ce wa wanda aka raina ƙwarai, Al'ummai suka ƙi shi, Bawa na masu mulki kuma, “Sarakuna za su gan ka a sake, Su kuma miƙe tsaye su ba ka girma, Shugabanni su kuma za su gani, Su rusuna har ƙasa su ba ka girma.” Wannan kuwa zai faru saboda Ubangiji, Allah Mai Tsarki na Isra'ila, ya zaɓi bawansa, Ya kuwa cika alkawaransa.