Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




W.Yah 3:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Don haka, sai ka tuna da abin da ka karɓa ka kuma ji, ka kiyaye shi, sa'an nan ka tuba. In ba za ka yi tsaro ba, zan zo kamar ɓarawo, ba kuwa za ka san a lokacin da zan auko maka ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Saboda haka, ka tuna fa, abin da ka karɓa ka kuma ji; ka yi biyayya da shi, ka kuma tuba. Amma in ba ka farka ba, zan zo kamar ɓarawo, ba kuwa za ka san lokacin da zan zo maka ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




W.Yah 3:3
24 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ka tuna da komawa bayan da ka yi fa, ka tuba, ka yi irin aikin da ka yi tun daga farko. In ba haka ba, zan zo a gare ka in kawar da fitilarka daga wurin zamanta, sai ko in ka tuba.


Duk da haka, ranar Ubangiji za ta zo kamar ɓarawo, sa'an nan sammai za su shuɗe da ƙara mai tsanani, dukkan abin da yake a cikinsu za su ƙone, su hallaka, ƙasa kuma da abubuwan da suke a kanta, duk za su ɓăce.


Domin ku da kanku kun sani sarai, ranar Ubangiji za ta zo ne kamar ɓarawo da dare.


(“Ga ni nan a tafe kamar ɓarawo! Albarka tā tabbata ga wanda yake a zaune a faɗake, yana saye da tufafinsa, don kada ya tafi tsirara, a ga tsiraicinsa.”)


Don haka, sai ku zauna a faɗake, don ba ku san ranar ba, ko kuwa sa'ar.”


Saboda haka, lalle ne mu ƙara mai da hankali musamman ga abubuwan da muka ji, don kada mu yi sakaci, su sulluɓe mana.


Ya Timoti, ka kiyaye abin da aka ba ka amana. Ka yi nesa da masu maganganun sāɓo na banza da wofi, da yawan musu da ake ƙarya, ake ce da shi ilimi.


Ku kula, ku zauna a faɗake, kuna addu'a, domin ba ku san sa'ar da lokacin zai yi ba.


Sa'an nan za ku tuna da mugayen hanyoyinku da ayyukanku marasa kyau. Za ku kuwa ji ƙyamar kanku saboda muguntarku da ayyukanku na banƙyama.


Waɗanda nake ƙauna, su nake tsawata wa, nake kuma horo. Saboda haka, sai ka himmantu ka tuba.


Ya ƙaunatattuna, wannan ita ce wasiƙa ta biyu da na rubuto muku, a kowaccensu kuwa na faɗakar da sahihan zukatanku ta hanyar tuni.


Ina zuwa da wuri. Ka riƙi abin da kake da shi kankan, kada wani ya karɓe maka kambinka.


Sai dai ku riƙi abin da kuke da shi kankan, har in zo.


A ganina daidai ne, muddin ina raye a cikin jikin nan, in riƙa faɗakar da ku ta hanyar tuni,


Ka yi koyi da sahihiyar maganar da ka ji daga gare ni, da bangaskiya da ƙauna da take ga Almasihu Yesu.


A nan za ku tuna da ayyukanku da dukan abubuwa da kuka ɓata kanku da su. Za ku ji ƙyamar kanku saboda mugayen abubuwa da kuka aikata.


Ka yi zaman tsaro, ka ƙarfafa abin nan da ya saura, yake kuma a bakin mutuwa, don ban ga aikinka cikakke ne ba a gaban Allahna.


“Ga shi kuwa, ina zuwa da wuri. Albarka tā tabbata ga wanda yake kiyaye maganar annabcin littafin nan.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ