Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




W.Yah 3:14 - Littafi Mai Tsarki

14 “Ka kuma rubuta wa mala'ikan ikkilisiyar da take a Lawudikiya haka, ‘Ga maganar tabbataccen nan, Amintaccen Mashaidi mai gaskiya, wanda ta wurinsa dukkan halittar Allah ta kasance.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

14 “Zuwa ga mala’ikan ikkilisiya a Lawodiseya, ka rubuta, Waɗannan su ne kalmomina Amin, amintaccen mashaidi mai gaskiya, da kuma mai mulkin halittar Allah.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




W.Yah 3:14
22 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Shi ne surar Allah marar ganuwa, magāji ne tun ba a halicci kome ba,


da kuma Yesu Almasihu Amintaccen Mashaidi, na farko a cikin masu tashi daga matattu, mai mulkin sarakunan duniya. Ɗaukaka da mulki su tabbata har abada abadin ga wanda yake ƙaunarmu, ya kuma ɓalle mana ƙangin zunubanmu ta wurin jininsa,


Shi ne kai ga jikin nan, wato Ikilisiya. Shi ne tushe, na farko a cikin masu tashi daga matattu, domin ta wurin kowane abu ya zama shi ne mafifici.


Domin dukan alkawaran Allah cikarsu a gare shi take, ta wurinsa ne kuma muke faɗar “Amin”, domin a ɗaukaka Allah.


“Ka kuma rubuta wa mala'ikan ikkilisiyar da take a Filadalfiya haka, ‘Ga maganar Mai Tsarkin nan, Mai gaskiya, wanda yake da mabuɗin Dawuda, wanda in ya buɗe, ba mai rufewa, in kuma ya rufe, ba mai buɗewa.


Ni ne Alfa, Ni ne Omega, Ni ne na Farko, Ni ne na Ƙarshe.”


Sai na ga sama ta dāre, sai ga wani farin doki! Mahayinsa kuwa ana ce da shi Amintacce, Mai Gaskiya, yana hukunci da adalci, yana kuma yaƙi.


Sa'an nan suka ce wa Irmiya, “Ubangiji mai gaskiya, mai aminci ya zama shaida a tsakaninmu, idan ba mu yi duk yadda Ubangiji Allahnka ya aiko ka gare mu ba.


Dukan wanda yake so ya roƙi albarka, sai ya roƙi Allah ya sa masa albarka, Allah da yake mai aminci ne. Dukan wanda zai sha rantsuwa, sai ya rantse da sunan Allah, Allah da yake mai aminci ne. Wahalan dā za su ƙare, za a kuwa manta da su.”


“Ni ce halittar farko da Ubangiji Ya fara halittawa daga cikin ayyukansa tuntuni.


Sai ya ce mini, “Wannan magana tabbatacciya ce, ta gaskiya ce kuma. Ubangiji, Allahn ruhohin annabawa ya aiko mala'ikansa, ya nuna wa bayinsa abin da lalle ne zai auku ba da daɗewa ba.”


Sai ya ce mini, “An gama! Ni ne Alfa, Ni ne Omega, Ni ne na Farko, Ni ne kuma na Ƙarshe. Duk mai jin ƙishirwa zan ba shi ruwa daga maɓuɓɓugar ruwan rai kyauta.


tana cewa, “Rubuta abin da ka gani a littafi, ka aika wa ikilisiyoyin nan bakwai, wato ta Afisa, da ta Simirna, da ta Birgamas, da ta Tayatira, da ta Sardisu, da ta Filadalfiya, da kuma ta Lawudikiya.”


“Sai ka rubuta wa mala'ikan ikkilisiyar da take a Afisa haka, ‘Ga maganar wadda take riƙe da taurarin nan bakwai a hannunsa na dama, wadda kuma take tafiya a tsakiyar fitilun nan bakwai na zinariya.


Sa'ad da aka karanta wasiƙar nan a gabanku, ku sa a karanta ta kuma a gaban ikilisiyar da take a Lawudikiya, ku kuma ku karanta tasu, wato ta Lawudikiyawa.


To, ina so ku san irin yawan shan faman da nake yi dominku, da waɗanda suke a Lawudikiya, da kuma duk waɗanda ba su taɓa ganina ba.


Na sa ya zama shugaba, da shugaban yaƙi na al'ummai, Ta wurinsa kuwa na nuna musu girmana.


“Ra'ubainu, kai ɗan farina ne, ƙarfina, Ɗan balagata, isasshe kuma, mafi ƙarfi duka cikin 'ya'yana.


Amma sai ya yarda ya ba ɗan farin, wato ɗan borar, za a ba shi riɓi biyu na dukan abin da yake da shi gama shi ne mafarin ƙarfinsa, yana da hakkin ɗan fari.”


Amintaccen mashaidi a ko yaushe yana faɗar gaskiya, amma marar aminci ba ya faɗar kome, sai ƙarairayi.


Dukan abubuwa sun kasance ta gare shi ne, ba kuma abin da ya kasance na abubuwan da suka kasance, sai ta game da shi.


Yesu ya amsa musu ya ce, “Ko na shaidi kaina, ai, shaidata tabbatacciya ce, domin na san inda na fito, da kuma inda za ni. Amma ku ba ku san inda na fito ba, ko kuma inda za ni.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ