Sa'an nan na duba, sai ga Ɗan Ragon nan a tsaye a kan Dutsen Sihiyona, akwai kuma mutum dubu ɗari da dubu arba'in da huɗu tare da shi, waɗanda aka rubuta sunansa, da sunan Ubansa, a goshinsu.
Duk wanda ya ci nasara, zan mai da shi ginshiƙi a Haikalin Allahna. Ba zai ƙara fita daga ciki ba, zan kuma rubuta sunan Allahna a jikinsa, da sunan Birnin Allahna, wato, Sabuwar Urushalima, mai saukowa daga wurin Allahna daga Sama, da kuma nawa sabon suna.
Gama yanzu kamar a madubi muke gani duhu duhu, a ranar nan kuwa za mu gani ido da ido. A yanzu sanina sama sama ne, a ranar nan kuwa zan fahimta sosai, kamar yadda aka fahimce ni sosai.
Ya Uba, ina so waɗanda ka ba ni, su ma su kasance tare da ni inda nake, su dubi ɗaukakata da ka yi mini, domin ka ƙaunace ni tun ba a halicci duniya ba.
Hamada za ta raira waƙa da sowa don murna, Za ta zama kyakkyawa kamar Dutsen Lebanon, Da dausayi kamar filayen Karmel da Sharon. Kowa zai ga mafificiyar ɗaukakar Allah, Ya ga girmansa da ikonsa.