Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




W.Yah 22:20 - Littafi Mai Tsarki

20 Shi wanda ya shaida abubuwan nan ya ce, “Hakika, ina zuwa da wuri.” Amin! Zo, ya Ubangiji Yesu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

20 Shi da ya shaida waɗannan abubuwa ya ce, “I, ina zuwa da wuri.” Amin. Zo, Ubangiji Yesu!

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




W.Yah 22:20
15 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Ga shi kuwa, ina zuwa da wuri. Albarka tā tabbata ga wanda yake kiyaye maganar annabcin littafin nan.”


shi Almasihu ma, da aka miƙa shi hadaya sau ɗaya tak, domin ya ɗauke zunuban mutane da yawa, zai sāke bayyana, bayyana ta biyu, ba a kan maganar kawar da zunubi ba, sai dai domin yă ceci waɗanda suke ɗokin zuwansa.


“Ga shi, ina zuwa da wuri, tare da sakamakon da zan yi wa kowa gwargwadon abin da ya yi.


Saura kuwa, sai sakamakon nan na aikin adalci, da aka tanadar mini, wanda Ubangiji, mahukunci mai adalci, zai ba ni a ranar nan, ba kuwa ni kaɗai ba, har da duk waɗanda suke ɗokin ganin bayyanarsa.


Duk wanda ba ya ƙaunar Ubangiji yă zama la'ananne. Ubangijinmu fa yana zuwa!


Ya kuma ce mini, “Kada ka rufe maganar annabcin littafin nan, domin lokaci ya kusa.


Sa'ad da wannan ya faru, kowa zai ce, “Shi Allahnmu ne! Mun dogara gare shi, ya kuwa cece mu. Shi ne Ubangiji. Mun dogara gare shi, yanzu kuwa muna da farin ciki domin ya cece mu!”


wanda ya shaidi Maganar Allah, da kuma shaidar Yesu Almasihu, har da dukan abin da ya gani.


Ina yi wa duk mai jin maganar annabcin littafin nan kashedi, in wani ya yi wani ƙari a kanta, Allah zai ƙara masa bala'in da aka rubuta a littafin nan.


Akwai waɗansu al'amura kuma masu yawa da Yesu ya aikata, in da za a rubuta kowannensu ɗaya ɗaya da ɗaya ɗaya, ina tsammani ko duniya kanta ba za ta iya ɗaukar littattafan da za a rubuta ba.


ni ne kuma Rayayye. Dā na mutu, amma ga shi a yanzu, ina a raye har abada abadin, ina kuwa da mabuɗan mutuwa da na Hades.


Ya ƙaunataccena, ka zo wurina da sauri, kamar batsiya, Ko sagarin kishimi a kan duwatsu inda kayan yaji yake tsirowa.


“Sauran lokaci kaɗan, Mai zuwan nan zai zo, ba kuwa zai yi jinkiri ba.


Saboda haka, sai ka tuba. In ba haka ba kuwa, zan zo a gare ka da wuri, in yaƙe su da takobin da yake a bakina.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ