Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




W.Yah 21:21 - Littafi Mai Tsarki

21 Ƙofofin gari goma sha biyun nan kuwa lu'ulu'u ne goma sha biyun, kowace ƙofa da lu'ulu'u guda aka yi ta, hanyar birnin kuwa zinariya ce zalla garau kamar ƙarau.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

21 Ƙofofi goma sha biyun nan lu’ulu’ai goma sha biyu ne, kowace ƙofa an yi ta da lu’ulu’u guda. Babban titin birnin kuwa an yi shi da zinariya zalla, yana kuma ƙyalli kamar madubi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




W.Yah 21:21
10 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Garun kuwa da yasfa aka gina shi, birnin kuma da zinariya zalla, garau kamar ƙarau.


Matar kuwa tana saye da tufafi masu ruwan jar garura, da kuma ja wur, ta ci ado da kayan zinariya, da duwatsun alfarma, da lu'ulu'u, tana a riƙe da ƙoƙon zinariya a hannunta, cike da abubuwan ƙyama, da ƙazantar fasikancinta.


ta tsakiyar hanyar birnin kuma, ta kowane gefen kogin, akwai itatuwan rai masu haihuwar 'ya'ya iri goma sha biyu, kowane wata suna haihuwa, ganyen itatuwan kuwa saboda lafiyar al'ummai ne.


“Kaito! Kaiton babban birnin nan! Wanda dā ya sa lallausan lilin, da tufafi masu ruwan jar garura, da kuma jan alharini, Wanda ya ci ado da kayan zinariya, da duwatsun alfarma, da lu'ulu'u!


Tsawon Wuri Mafi Tsarki na can ciki kamu ashirin ne, fāɗinsa kamu ashirin, tsayinsa kuma kamu ashirin. Ya dalaye shi da zinariya tsantsa. Ya kuma yi bagadensa da itacen al'ul.


A gaban kursiyin kuwa akwai wani abu kamar bahar na gilas, garau yake kamar ƙarau. Kewaye da kursiyin kuma, ta kowane gefensa, da waɗansu rayayyun halitta guda huɗu, masu idanu ta ko'ina, gaba da baya.


Shi wanda ya yi mini magana kuwa yana da sandar awo ta zinariya, domin ya auna birnin, da ƙofofinsa, da garunsa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ