Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




W.Yah 21:10 - Littafi Mai Tsarki

10 Sai ya ɗauke ni, Ruhu yana iza ni, ya kai ni wani babban dutse mai tsawo, ya nuna mini tsattsarkan birnin Urushalima yana saukowa daga Sama daga wurin Allah,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

10 Ya kuwa ɗauke ni cikin Ruhu zuwa wani babban dutse mai tsayi, ya kuma nuna mini Birni Mai Tsarki, Urushalima, tana saukowa daga sama, daga Allah.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




W.Yah 21:10
17 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai na ga tsattsarkan birni kuma, Sabuwar Urushalima, tana saukowa daga Sama daga wurin Allah, shiryayyiya kamar amaryar da ta yi ado saboda mijinta.


Ruhu kuwa ya ɗauke ni a cikin wahayi, ya kai ni Kaldiya wurin 'yan zaman talala. Sa'an nan wahayin da na gani ya rabu da ni.


Sai ya ɗauke ni ya tafi da ni zuwa jeji, Ruhu yana iza ni, sai na ga wata mace a kan wata dabba ja wur, duk jikin dabbar sunayen saɓo ne, tana kuma da kawuna bakwai, da ƙaho goma.


A ranar Ubangiji ya zamana Ruhu ya iza ni, sai na ji wata murya mai ƙara a bayana kamar ta ƙaho,


Da suka fito daga ruwan, Ruhun Ubangiji ya fauce Filibus, bābān kuma bai ƙara ganinsa ba. Sai ya yi ta tafiya tasa yana farin ciki.


Sai Ruhu ya ɗaga ni sama, ya kai ni ƙofar gabas ta Haikalin Ubangiji wadda dake fuskantar gabas. Sai ga mutum ashirin da biyar a bakin ƙofar. A cikinsu na ga Yazaniya ɗan Azzur, da Felatiya ɗan Benaiya, shugabannin jama'a.


Sai ya miƙa hannu, ya kama zankon kaina. Ruhu kuma ya ɗaga ni bisa tsakanin sama da ƙasa, ya kai ni Urushalima cikin wahayi zuwa ƙofar farfajiya ta ciki, wadda take fuskantar arewa, inda mazaunin siffa ta tsokano kishi yake.


Nan da nan kuwa Ruhu ya iza ni, sai ga wani kursiyi a girke a Sama, da wani a zaune a kai.


Sai Ruhu ya ɗaga ni, ya kuma tafi da ni, na kuwa tafi da baƙin ciki, ina jin zafi a ruhuna. Ikon Ubangiji yana tare da ni da ƙarfi.


Rabuwata da kai ke da wuya, sai Ruhun Ubangiji ya kai ka wurin da ban sani ba, don haka, in na tafi na faɗa wa Ahab, in bai same ka ba, to, ni zai kashe, ko da yake ni baranka, tun ina saurayi nake tsoron Ubangiji.


suka kuma ce masa, “Yanzu fa, ga mu mu hamsin ƙarfafa. Bari mu tafi mu nemo maigidanka, mai yiwuwa ne Ruhun Ubangiji ya ɗauke shi, ya jefa shi kan wani dutse, ko cikin wani kwari.” Elisha ya ce, “Kada ku tafi.”


Amma Urushalima ta sama, ai 'ya ce, ita ce kuma uwarmu.


Duk wanda ya ci nasara, zan mai da shi ginshiƙi a Haikalin Allahna. Ba zai ƙara fita daga ciki ba, zan kuma rubuta sunan Allahna a jikinsa, da sunan Birnin Allahna, wato, Sabuwar Urushalima, mai saukowa daga wurin Allahna daga Sama, da kuma nawa sabon suna.


amma kada ka auna harabar Haikalin, ka ƙyale ta, domin an ba da ita ga al'ummai, za su tattake tsattsarkan birnin nan har wata arba'in da biyu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ