W.Yah 20:11 - Littafi Mai Tsarki11 Sa'an nan na ga wani babban kursiyi fari, da wanda yake a zaune a kai, sai sama da ƙasa suka guje wa Zatinsa, suka ɓace. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202011 Sa’an nan na ga babban farin kursiyi da kuma wannan da yake zama a kansa. Duniya da sararin sama kuwa suka ɓace daga gabansa, babu wuri kuwa dominsu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa'an nan baƙin ƙarfen, da yumɓun, da tagullar, da azurfar, da zinariyar suka ragargaje gaba ɗaya, duka suka zama kamar ƙaiƙayi na masussuka da kaka. Iska kuwa ta kwashe su ta tafi da su, har ba a iya ganin ko alamarsu. Amma wannan dutse da ya buge mutum-mutumin ya girke, ya zama babban dutse ya cika duniya duka.