Lalle ne a kullum mu gode wa Allah saboda ku, 'yan'uwa, haka kuwa ya kyautu, da yake bangaskiyarku haɓaka take yi ƙwarai da gaske, har ma ƙaunar kowane ɗayanku ga juna ƙaruwa take yi.
Amma ga waɗansu laifofinka kaɗan. Akwai waɗansu a cikinku, da suke bin koyarwar Bal'amu, wanda ya koya wa Balak ya sa Isra'ilawa laifi, don su ci abincin da aka yi wa gumaka sadaka, su kuma yi fasikanci.
Amma ga laifinka, wato, ka haƙurce wa matar nan Yezebel, wadda take ce da kanta annabiya, take kuma koya wa bayina, tana yaudararsu, su yi fasikanci, su kuma ci abincin da aka yi wa gumaka hadaya.