Don haka, sai ka tuna da abin da ka karɓa ka kuma ji, ka kiyaye shi, sa'an nan ka tuba. In ba za ka yi tsaro ba, zan zo kamar ɓarawo, ba kuwa za ka san a lokacin da zan auko maka ba.
Ga shi, zai zo a cikin gajimare, kowa zai gan shi, har da waɗanda suka soke shi, duk kabilan duniya kuma za su yi kuka a kansa. Wannan haka yake. Amin.
amma Almasihu mai aminci ne, yana mulkin jama'ar Allah a kan shi Ɗa ne, mu ne kuwa jama'arsa, muddin mun tsaya gabanmu gaɗi, muna gadara da begenmu ƙwarai.
Duk da haka, ranar Ubangiji za ta zo kamar ɓarawo, sa'an nan sammai za su shuɗe da ƙara mai tsanani, dukkan abin da yake a cikinsu za su ƙone, su hallaka, ƙasa kuma da abubuwan da suke a kanta, duk za su ɓăce.
Don haka, kada ku yanke wani hukunci tun lokaci bai yi ba, kafin komowar Ubangiji, wanda zai tone al'amuran da suke ɓoye a duhu, ya kuma bayyana nufin zukata. A sa'an nan ne, Allah zai yaɓa wa kowa daidai gwargwado.
Sai ɗaya daga cikinsu, mai suna Agabas, ya miƙe tsaye, ya yi faɗi da ikon Ruhu, cewa za a yi wata babbar yunwa, a duniya duka, an yi ta kuwa a zamanin Kalaudiyas.