Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




W.Yah 2:23 - Littafi Mai Tsarki

23 Zan kashe 'ya'yanta tashi ɗaya, dukan ikilisiyoyi kuma za su sani Ni ne mai fayyace birnin zuciya. Zan kuma saka wa kowannenku gwargwadon aikinsa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

23 Zan kashe ’ya’yanta. Sa’an nan dukan ikkilisiyoyi za su san cewa ni ne mai bincika zukata da tunani, zan kuwa sāka wa kowannenku gwargwadon ayyukansa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




W.Yah 2:23
39 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Domin Ɗan Mutum zai zo da ɗaukakar Ubansa tare da mala'ikunsa. A sa'an nan ne zai sāka wa kowane mutum gwargwadon aikinsa.


Ka tsai da muguntar mugaye, Ina roƙonka, ka sāka wa mutanen kirki. Kai Allah mai adalci ne, Kana kuwa auna tunanin mutane, da marmarinsu.


Amma shi mai fayyace zukatanmu ya san abin da Ruhu yake niyya, domin bisa ga nufin Allah ne Ruhu yake yi wa tsarkaka roƙo.


Sai suka yi addu'a, suka ce, “Ya Ubangiji, masanin zuciyar kowa, a cikin waɗannan mutum biyu ka nuna wanda ka zaɓa,


Da yake kuna kiransa Uba a wajen addu'a, shi da yake yi wa kowa shari'a gwargwadon aikinsa, ba zaɓe, sai ku ƙarasa lokacin baƙuncinku, kuna tsoronsa.


Amma ya Ubangiji Mai Runduna, mai shari'ar adalci, Kakan gwada zuciya da tunani, Ka yarda mini in ga sakayyar da za ka yi mini a kansu, Gama a gare ka na danƙa maganata.


Ni Ubangiji nakan bincike tunani, In gwada zuciya, Domin in sāka wa kowane mutum gwargwadon al'amuransa, Da kuma gwargwadon ayyukansa.


Ya Ubangiji Mai Runduna, mai gwada adali, Mai ganin zuciya duk da tunani, Ka sa in ga sakayyar da za ka yi musu, Gama a gare ka nake kawo ƙarata.”


Madawwamiyar ƙauna, ta Ubangiji ce. Kai kanka, ya Ubangiji, kake sāka wa Kowane mutum bisa ga ayyukansa.


Hakika ka gane, Domin ka san asirin tunanin mutane.


sa'an nan za ka ji daga wurin zamanka a Sama, ka yi gafara, ka kuwa sāka wa kowa bisa ga al'amuransa, wanda ka san zuciyarsa, gama kai kaɗai ne ka san zukatan mutane,


Amma Ubangiji ya ce masa, “Kada ka kula da kyan tsarinsa, ko tsayinsa, domin ba shi nake so ba, gama yadda Ubangiji yake gani, ba haka mutum yake gani ba. Mutum yakan dubi kyan tsari ne kawai, amma Ubangiji yakan dubi zuciya.”


Sai na ga matattu manya da yara, a tsaitsaye a gaban kursiyin, aka kuma buɗe littattafai. Sai kuma aka buɗe wani littafi, wanda yake shi ne Littafin Rai. Aka kuwa yi wa matattu shari'a bisa ga abin da yake a rubuce a cikin littattafan, gwargwadon aikin da suka yi.


Ba wata halittar da za ta iya ɓuyar masa, amma kowane abu a fili yake, a shanye sosai a gaban idon wannan da za mu ba da lissafi a gabansa.


Don lalle ne a gabatar da mu duka, a gaban kursiyin shari'a na Almasihu, domin kowa yă sami sakamakon abin da ya yi tun yana tare da wannan jiki, ko mai kyau ne, ko kuma marar kyau.


Ka jarraba ni ka auna ni, ya Ubangiji, Ka gwada muradina da tunanina.


Da yake na sani, ya Allahna, kakan gwada zuciya, kana ƙaunar gaskiya, bisa ga amincewar zuciyata, da yardar rai, na miƙa maka dukan waɗannan abubuwa. Ina murna da ganin jama'arka waɗanda suke nan a tattare, sun kawo maka sadakokinsu da yardar rai.


“Kai kuwa ɗana Sulemanu, sai ka san Allah na tsohonka, ka bauta masa da zuciya ɗaya, da kuma yardar rai, gama Ubangiji mai binciken dukan zukata ne, ya kuma san kowane irin nufi da tunani. Idan ka neme shi, za ka same shi, in kuwa ka rabu da shi, shi ma zai yi watsi da kai har abada.


Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikilisiyoyi. Duk wanda ya ci nasara, mutuwa ta biyu ba za ta cuce shi ba ko kaɗan.’ ”


Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikilisiyoyi. Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi izinin cin 'ya'yan itacen rai, wanda yake a cikin Firdausin Allah.’ ”


Don haka kowannenmu zai faɗi abin da shi da kansa ya yi, a gaban Allah.


Yesu ya faɗa masa, faɗa ta uku, “Bitrus ɗan Yahaya, kana sona?” Sai Bitrus ya yi baƙin ciki don a faɗar nan ta uku ya ce masa, “Kana sona?” Shi kuwa ya ce masa, “Ya Ubangiji, ai, ka san kome duka, ka kuwa sani ina sonka.” Yesu ya ce masa, “Ka yi kiwon tumakina.


Sauranku za su ji, su ji tsoro, ba za a ƙara aikata irin wannan mugunta ba.


Sa'an nan duk jama'a za su ji, su kuwa ji tsoro. Ba za su ƙara yin izgilanci ba kuma.”


Da haka nan dukan Isra'ilawa za su ji, su ji tsoro, har da ba za su ƙara aikata mugun abu irin wannan a cikinku ba.


Da na duba, ga doki kili, sunan mahayinsa kuwa Mutuwa, Hades kuma tana biye da shi. Sai aka ba su iko a kan rubu'in duniya, su yi kisa da takobi, da yunwa, da annoba, da kuma namomin jeji na duniya.


Sa'an nan, sai mutanen garin su jajjefe shi da duwatsu har ya mutu. Ta haka za ku kawar da mugunta daga cikinku. Dukan Isra'ilawa za su ji, su ji tsoro.”


Ku yi kururuwa, ku mazaunan Maktesh, Gama 'yan kasuwa sun ƙare, An kuma datse dukan waɗanda suke awon azurfa.


Sai ya ce musu, “Ku ne masu baratar da kanku a gaban mutane. Amma Allah ya san zukatanku. Abin da mutane suke girmamawa ƙwarai, ai, abin ƙyama ne a gun Allah.


Sai teku ta ba da matattun da suke a cikinta, mutuwa da Hades kuma sun ba da matattun da suke a gare su, aka kuwa yi wa kowa shari'a gwargwadon aikin da ya yi.


“Ga shi, ina zuwa da wuri, tare da sakamakon da zan yi wa kowa gwargwadon abin da ya yi.


Me kuma ni Dawuda zan ƙara ce maka, a kan girman da ka ba bawanka? Gama ka san bawanka.


Ya yiwu Allah ya bar shi ya yi zamansa lafiya, Amma a kowane lokaci zai sa ido a kansa.


Sai Yesu ya ce mata, “Je ki, ku zo da mijinki.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ