Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




W.Yah 19:2 - Littafi Mai Tsarki

2 Don hukuncinsa daidai yake, na adalci ne, Ya hukunta babbar karuwar nan wadda ta ɓata duniya da fasikancinta, Ya kuma ɗauki fansar jinin bayinsa a kanta.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 gama hukuncinsa daidai ne, mai adalci kuma. Ya hukunta babbar karuwan nan wadda ta ɓata duniya da zinace zinacenta. Ya rama jinin bayinsa a kanta.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




W.Yah 19:2
16 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Ya ku al'ummai, ku yabi jama'arsa, Gama zai rama wa bayinsa saboda jininsu, Zai ɗauki fansa a kan magabtansa, Zai tsarkake ƙasar jama'arsa.”


Sai suka ta da murya da ƙarfi suka ce, “Ya Ubangiji Mamallaki, Mai Tsarki, Mai Gaskiya, sai yaushe ne za ka yi hukunci, ka ɗaukar mana fansar jininmu a gun mazaunan duniya?”


Ki yi farin ciki saboda an yi masa haka, ya sama! Ku yi farin ciki, ku tsarkaka da manzanni da annabawa, domin Allah ya rama muku abin da ya yi muku!”


Sakayya da ɗaukar fansa nawa ne, A lokacin ƙafarsu za ta zame, Gama ranar masifarsu ta kusa, Hallakarsu za ta zo da sauri.’


Dukkan al'ummai sun yi tsananin jarabar yin fasikanci da ita, Sarakunan duniya kuma sun yi fasikanci da ita, Attajiran duniya kuma sun arzuta da almubazzarancinta.”


Suna raira waƙar da Musa bawan Allah ya yi, da kuma wadda ake yi wa Ɗan Ragon nan, suna cewa, “Ayyukanka manya ne, masu banmamaki, Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki! Hanyoyinka na adalci ne, na gaskiya ne kuma, Ya Sarkin al'ummai.


Daidai ne a bauta wa Ubangiji, A ci gaba da yi har abada. Duk abin da Ubangiji ya hukunta daidai ne, A kullum hukuntan Ubangiji daidai suke.


Ya Ubangiji, kai ne Allahna, Zan ɗaukaka ka, in yabi sunanka. Ka aikata al'amura masu banmamaki, Ka tafiyar da su da aminci, Wato bisa ga shirin da ka yi tuntuni.


“Shi Dutse ne, aikinsa kuma cikakke ne, Gama dukan hanyoyinsa masu adalci ne. Allah mai aminci ne, babu rashin gaskiya a gare shi, Shi mai adalci ne, nagari ne kuma.


Za ka hallaka gidan Ahab, maigidanka, domin in ɗau fansar jinin annabawa bayinsa, da fansar jinin sauran bayin Ubangiji a kan Yezebel.


Amma majalisa za ta zauna ta yanke shari'a, za a karɓe mulkinsa, a hallaka shi har abada.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ