Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




W.Yah 18:10 - Littafi Mai Tsarki

10 za su tsaya a can nesa, don tsoron azabarta, su ce, “Kaitonka! Kaitonka, ya kai babban birni! Ya kai birni mai ƙarfi, Babila! A sa'a ɗaya hukuncinka ya auko.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

10 Don tsoron ganin azabarta za su tsaya daga nesa, su yi kuka suna cewa, “ ‘Kaito! Kaito, ya birni mai girma. Ya ke Babilon, birni mai iko! Cikin sa’a guda hallakarki ta zo!’

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




W.Yah 18:10
17 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Har suka tula wa kansu ƙasa suna ta kuka, suna baƙin ciki, suna kururuwa, suna cewa, “Kaito! Kaiton babban birnin nan! Wanda duk masu jiragen ruwa a bahar suka arzuta da ɗumbun dukiyarsa, A sa'a ɗaya ya hallaka.


Saboda haka, bala'inta zai aukar mata rana ɗaya, Mutuwa, da baƙin ciki, da yunwa. Za a kuma ƙone ta, Domin Ubangiji Allah da yake hukunta ta Mai Ƙarfi ne.”


Sai kuma mala'ika na biyu ya biyo, yana cewa, “Ta fāɗi! Babila mai girma ta fāɗi! Ita da ta zuga dukkan al'ummai su yi tsananin jarabar yin fasikanci da ita.”


Haka Ubangiji Allah Mai Runduna ya ce, “Za a yi kuka, a yi kururuwa a titunan birninku saboda azaba. Daga ƙauyuka za a kirawo mutane Su zo su yi makokin. Waɗanda suka mutu, tare da masu makoki da aka ijarar da su.


Taku ta ƙare a wannan rana! Gama ranar Ubangiji ta kusa, Halaka daga wurin Maɗaukaki ta zo.


Ƙahonin nan goma kuwa da ka gani, sarakuna goma ne, waɗanda ba a naɗa ba tukuna, amma sa'a ɗaya tak, za a ba su ikon yin mulki tare da dabbar.


Kaito, gama wannan babbar rana ce, Ba kuma kamarta, Lokaci ne na wahala ga Yakubu, Duk da haka za a cece shi daga cikinta.”


Farat ɗaya sai ga su sun zo! Suna tafe a kan dawakai biyu biyu. Sai mai tsaro ya ba da labari cewa, “Babila ta fāɗi! Dukan gumakan da suke yi wa sujada an ragargaza su har ƙasa.”


Sai Isra'ilawa duka waɗanda suke kewaye da su suka gudu saboda kururuwansu, suka ce. “Mu mā gudu, kada kuma ƙasa ta haɗiye mu.”


Amma ba da jimawa ba, a rana ɗaya Dukan waɗannan al'amura za su faru. Kome sihirin da za ki yi, Za ki rasa 'ya'yanki, ki kuwa zama gwauruwa.


“Zukatan al'ummai da yawa za su ɓaci, sa'ad da na baza labarin halakarka a ƙasashen da ba ka sani ba.


a kuma bar gawawwakinsu a kan hanyar babban birnin nan da ake kira Saduma da Masar ga ma'ana ta ruhu, a inda aka gicciye Ubangijinsu.


Babban birnin nan kuwa ya rabu gida uku, biranen al'ummai kuma suka fāɗi. Sai Allah ya tuna da Babila mai girma, don ya sa ta, ta sha fushinsa mai tsananin gaske.


suna kururuwa da suka ga hayaƙin ƙunarsa, suna cewa, “Wane birni ne ya yi kama da babban birnin nan?”


Sai wani ƙaƙƙarfan mala'ika ya ɗauki wani dutse kamar babban dutsen niƙa, ya jefa a teku, ya ce, “Haka za a fyaɗa Babila babban birni, da ƙarfi, ba kuwa za a ƙara ganinta ba.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ