W.Yah 17:8 - Littafi Mai Tsarki8 Dabbar nan da ka gani, wadda dā take nan, a yanzu kuwa ba ta, za ta hawo ne daga ramin mahallaka, ta je ta hallaka, mazaunan duniya kuma waɗanda tun a farkon duniya, ba a rubuta sunayensu a Littafin Rai ba, za su yi mamakin ganin dabbar, don dā tana nan, a yanzu ba ta, za ta kuma dawo. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20208 Dabbar da ka gani, a dā ta taɓa kasancewa, a yanzu, ba ta, za tă kuma fito daga Abis zuwa ga hallakarta. Mazaunan duniya waɗanda ba a rubuta sunayensu a littafin rai tun kafin halittar duniya ba za su yi mamaki sa’ad da suka ga dabbar, domin a dā ta taɓa kasancewa, yanzu kuwa ba ta, duk da haka za tă dawo. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |