W.Yah 17:4 - Littafi Mai Tsarki4 Matar kuwa tana saye da tufafi masu ruwan jar garura, da kuma ja wur, ta ci ado da kayan zinariya, da duwatsun alfarma, da lu'ulu'u, tana a riƙe da ƙoƙon zinariya a hannunta, cike da abubuwan ƙyama, da ƙazantar fasikancinta. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20204 Macen tana saye da tufafi masu ruwan ja da shunayya, tana ƙyalli da zinariya, duwatsu masu daraja da kuma lu’ulu’ai. Tana riƙe da kwaf na zinariya a hannunta, cike da abubuwa masu banƙyama da kuma ƙazantar zinace zinacenta. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
“Mutane suna yin abin da suka ga dama. Suna kashe bijimi domin hadaya, ko su yi hadaya da mutum. Sukan yi hadaya da ɗan rago, ko kuwa su karye wuyan kare. Sukan miƙa hadaya ta hatsi, ko kuwa su miƙa jinin alade. Suna miƙa turare, ko kuwa su yi addu'a ga gumaka. Suna jin daɗin al'amuran banƙyama a lokacin yin sujada.