Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




W.Yah 16:19 - Littafi Mai Tsarki

19 Babban birnin nan kuwa ya rabu gida uku, biranen al'ummai kuma suka fāɗi. Sai Allah ya tuna da Babila mai girma, don ya sa ta, ta sha fushinsa mai tsananin gaske.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

19 Babban birnin ya rabu kashi uku, biranen al’ummai kuma suka rurrushe. Allah ya tuna da Babilon Mai Girma ya kuma ba ta kwaf cike da ruwan inabin fushinsa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




W.Yah 16:19
15 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Domin zunubanta sun yi tsororuwa, sun kai har Sama, Allah kuwa ya tuna da laifofinta.


za su tsaya a can nesa, don tsoron azabarta, su ce, “Kaitonka! Kaitonka, ya kai babban birni! Ya kai birni mai ƙarfi, Babila! A sa'a ɗaya hukuncinka ya auko.”


Matar nan da ka gani kuwa, ita ce babban birnin da yake mulkin sarakunan duniya.”


Sai wani ƙaƙƙarfan mala'ika ya ɗauki wani dutse kamar babban dutsen niƙa, ya jefa a teku, ya ce, “Haka za a fyaɗa Babila babban birni, da ƙarfi, ba kuwa za a ƙara ganinta ba.


Sai ya yi kira da murya mai ƙarfi, ya ce, “Ta fāɗi! Babila mai girma ta fāɗi! Ta zama mazaunin aljannu, Matattarar kowane baƙin aljani, Da kowane irin ƙazamin tsuntsu, abin ƙyama.


A goshinta kuma an rubuta wani sunan asiri, “Babila mai girma, uwar karuwai, uwar abubuwa masu banƙyama na duniya.”


sai ya ce, “Ashe, wannan ba ita ce Babila babba wadda ni da kaina na gina, da ƙarfin ikona don ta zama fādar sarauta, don darajar ɗaukakata?”


a kuma bar gawawwakinsu a kan hanyar babban birnin nan da ake kira Saduma da Masar ga ma'ana ta ruhu, a inda aka gicciye Ubangijinsu.


Zan sa masu zaluntarku su karkashe juna, Za su yi māye, da kisankai, da fushi. Sa'an nan dukan 'yan adam za su sani, ni ne Ubangiji, Wanda ya cece ku, ya fanshe ku. Za su sani ni ne Allah Mai Iko Dukka na Isra'ila.”


Sai ɗaya daga cikin mala'ikun nan bakwai masu tasoshin nan bakwai, ya zo ya yi mini magana, ya ce, “Zo in nuna maka hukuncin da za a yi wa babbar karuwar nan, wadda take zaune a bisa ruwa mai yawa,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ