Za su yi yaƙi da Ɗan Ragon, Ɗan Ragon kuwa zai cinye su, shi da waɗanda suke tare da shi, kirayayyu, zaɓaɓɓu, amintattu, domin shi ne Ubangijin iyayengiji.”
Da duk muka fāɗi, sai na ji wata murya tana ce mini da yahudanci, ‘Shawulu, Shawulu, don me kake tsananta mini? Da wuya a gare ka ka yi ta shuri bisa a kan tsini.’
Ni kuwa zan jawo Sisera, shugaban sojojin Yabin, da karusansa, da ƙungiyoyin sojojinsa ya yi karo da kai a Kogin Kishon, zan kuwa bashe shi a hannunka.’ ”
Duk da haka Yosiya bai yarda ya koma ba, sai ya ɓad da kama don ya yi yaƙi da shi. Bai yarda da magana wadda Allah ya faɗa wa Neko ba, sai suka kama yaƙi a filin Magiddo.