Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




W.Yah 16:1 - Littafi Mai Tsarki

1 Sai na ji wata murya mai ƙara daga Haikalin, tana ce wa mala'ikun nan bakwai, “Ku je ku juye tasoshin nan bakwai na fushin Allah a kan duniya.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Sai na ji wata babbar murya daga haikalin tana ce wa mala’iku bakwai nan, “Ku tafi ku zuba kwanoni bakwai nan na fushin Allah a kan duniya.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




W.Yah 16:1
17 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Domin haka ni Ubangiji na ce, Ku jira ni zuwa ranar da zan tashi in yi tuhuma. Gama na ƙudura zan tattara al'umman duniya, da mulkoki, Don in kwarara musu hasalata Da zafin fushina, Gama zafin kishina Zai ƙone dukan duniya.


Na kuma ga wata alama a Sama, mai girma, mai banmamaki, mala'iku bakwai masu bala'i bakwai, waɗanda suke bala'in ƙarshe, don su ne iyakacin fushin Allah.


Ka kwarara hasalarka a kan sauran al'umma da ba su san ka ba, Da a kan jama'ar da ba su kiran sunanka, Gama sun cinye Yakubu, Sun cinye shi, sun haɗiye shi, Sun kuma mai da wurin zamansa kufai.”


Mala'ika na bakwai ya juye abin da yake a tasarsa a sararin sama, sai aka ji wata murya mai ƙara daga Haikali, wato, daga kursiyin, ta ce, “An gama!”


Ka yi fushi da al'umman da ba su yi maka sujada, Ka yi fushi da jama'ar da suka ƙi ka!


Sai Ubangiji ya ce wa mutumin da yake saye da rigar lilin. “Ka shiga ƙarƙashin ƙafafun kerubobin, ka cika tafin hannunka da garwashin wuta wanda yake tsakanin kerubobin, ka watsa bisa kan birnin.” Na kuwa ga ya tafi.


Sai kuma wani mala'ika ya fito daga bagadin ƙona turare, wato, mala'ikan da yake da iko da wutar, ya yi magana da murya mai ƙarfi da wannan mai kakkaifan lauje, ya ce, “Ka sa laujenka ka yanke nonnan inabin zuwa duniya, don inabin ya nuna.”


Sai mala'ika ya fito daga Haikalin, yana magana da murya mai ƙarfi da wanda yake a zaune a kan gajimaren, yana cewa, “Ka sa laujenka ka yanke, don lokacin yanka ya yi, amfanin duniya ya nuna sarai.”


Ka tafi yanzu, ka fāɗa wa Amalekawa da yaƙi. Ka hallakar da dukan abin da suke da shi. Kada ka rage kome, ka karkashe su dukka, da mata da maza, da yara da jarirai, da takarkarai, da tumaki, da raƙuma, da jakai.”


ya kuma umarce ka ka tafi ka hallakar da waɗannan mugayen mutane, wato Amalekawa. Ya faɗa maka ka yi yaƙi, har ka hallaka su ƙaƙaf, kada ka rage ko guda ɗaya.


Saboda haka na kwarara musu fushina, na ƙone su da wutar hasalata, na ɗora alhakin ayyukansu a bisa kawunansu, ni Ubangiji Allah na faɗa.”


Sa'an nan aka buɗe Haikalin nan na Allah da yake a Sama, aka kuma ga akwatin alkawarinsa a Haikalinsa. Sai aka yi ta walƙiya da kururuwa, da aradu, da rawar ƙasa, da ƙanƙara manya manya.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ