Waɗanda suka ragu cikin Isra'ila, Ba za su aikata mugunta ba, Ba kuma za su faɗi ƙarya ba, Gama harshen ƙarya ba zai kasance a bakinsu ba. Za su yi kiwo, su kwanta, Ba wanda zai tsorata su.”
Amma a yanzu ya sulhunta ku ta hanyar jikinsa na mutuntaka, wato, ta wurin mutuwarsa, domin ya miƙa ku tsarkakakku, marasa aibu, marasa abin zargi kuma a gabansa.
Sai shugabannin, da su muƙaddasan suka nemi Daniyel da laifi game da ayyukan mulki, amma ba su sami laifin da za su tuhume shi da shi ba, domin shi amintacce ne, ba shi da kuskure ko ha'inci.
Koyarwar gaskiya tana cikin bakinsa, ba a sami kuskure a bakinsa ba. Ya yi tafiya tare da ni da salama da gaskiya. Ya kuwa juyo da mutane da yawa daga mugunta.
balle fa jinin Almasihu wanda ya miƙa kansa marar aibu ga Allah, ta wurin Madawwamin Ruhu, lalle zai tsarkake lamirinmu daga barin ibada marar tasiri, domin mu bauta wa Allah Rayayye.